Ga dukkan alamu a bikin Babbar Sallar bana raguna sun gagari kundela bisa la’akari da yadda farashinsu ya ninninka fiye da na ‘yan shekarun da suka gabata. Wannan kuwa ya auku ne sakamakon yadda ake samun hauhawar farashin kayan masarufi da sauran abubuwa na rayuwa a ‘yan kwanakin nan.
Al’amarin ya yi matukar tayar da hankalin masu karamin karfi. A bara an yi kuka da yadda farashin rago ya fi karfin talaka amma a wannan shekarar lamarin raguna sun gagari kundila, layya ta zama sai wane da wane.
Wasu wakalinmu sun duba mana yadda farashin yake a garuruwansu, ga kuma rahoton da suka aiko mana dangane da wannan dan karen tsada da ragunan suka yi.
Babbar Sallar bana, Sallar da Yara ke yawan yi wa wakar cewa, “Gobe sallah za mu ci naman damushere” kila a wannan karon Sallar za a yi ta kadamus. Musamman ganin yadda dabbobi Suka yi matukar tsada, wadda a wannan Shekarar Kafi Zurun ma na neman gagarar matsakaicin Talaka.
Irin Kano birni ne da ke yin cikar kwari a duk lokutan sallah irin wanan, amma a wannan lokaci sakamakon matsin tattalin arziki da tsadar dabbobi yasa har yanzu Kasuwannin kamar an yi ruwa an dauke, Kasuwar Dabbobi ta Unguwa uku ita ce Kasuwar da a hukumance ke gudanar da harkokin ta bisa Sahalewar Gwamnati, amma sauran kasuwannin duk suna cin tasu Kasuwar ne a matsayin ‘yan share wuri zauna kawai.
Yanzu haka duk inda ka zaga a kwaryar birnin zaka tarar da an bude Kasuwannin tsaye da aka kasa dabbobi domin neman masu saya, Baya ga dabbobin da ake shiga da su lungu da sakon Kasuwanni da rukunin ungawanin masu hannu da shuni ko za a dace da mai saye.
Kamar yadda LEADERSHIP HAUSA ta samu zarafin tattaunawa da wani dillalin dabbobi a Kasuwar Dabbobi ta Unguwa Uku Malam Idi Sheka cewa ya yi, “Mukam har yanzu mun kasa rarrabewa tsakanin barcin makaho, ga dai dabbobi kamar abayar kyauta, sai dan karen tsada ga kuma rashin masaya, dan dalon sa wanda a shekarun baya idan ka baiwa wani irinsa ma ce a zai yi bai isa layya ba, amma yanzu shi ne farashinsa ya fara daga Dubu 150,000.00 zuwa sama yayin da turkakken ake maganar Miliyon daya harda doriya.
Wani abu da yafi daukar hankali shi ne yadda ake kyautata zaton kasuwar Rakuma ce za ta fi ci a wannan karon, domin da yawa Rakuna sunfi shanu rangwame. Haka lamarin yake a bangaren Raguna, Wanda Idon LEADERSHIP ya gane mata Ragon Naira Dubu 600,000.00 zuwa sama. Yayin da ake samun can matunbirin Rakumin Naira Dubu dari da doriya.
Duk da cewa Ma’aikatan Gwamnatin sai cikin wannan satin suka fara jin alert, hakan yasa ake ganin masu dan guzuri ka iya tunkarar Kafi Zuru ko kuma neman shiga watanda domin samun dan abinda za a dan jefa a miyar Salla.
Sai dai kuma kasuwar masu sayar da kaskon suya da matsamin Nama sun baje kolinsu bisa fatan suma suci kasuwarsu, Haka lamarin yake bangaren masu albasa sun kasa sun tsare itama albasar tana dan Karen tsada duk domin gabatowar Sallar.
Suma ‘yan siyasar da irin wannan lokaci suke rabon raguna ga abokan siyasarsu, masoya da Kuma masu rabo, Amma har yanzu shiru kake hi Wai Malam yaci shirwa, bil hasali ma tuni suke ta sulalewa zuwa Kasa Mai tsarki domin gudanar da aikin Hajjin.
Al’umma Su Yi Hidima Daidai Karfinsu
Wani Malamin addnin Musuluncin a garin Samarun Zariya mai suna Malam Lukman Alfah ya bayyana cewa, yakamata al’umma su fahinci cewa, al’amarin layya kamar sauran ibadojin da Allah (SWT) Ya dora mana suna da ka’doji ba wai an barsu mu yi kara zube ba ne, Malam Lukman yana magana ne a kan yadda mutane ke kukan yadda raguna suka yi tashin gwauron zabi, ya ce, Layya ba wajibi bane a kan Musulmi amma Sunnah ce mai karfi da ake so Musulmai su karfafa yinta, ya kuma kamata al’umma su dauki lamarin layya daidai karfinsu, “Yin layya da Rago shi ne almuhimm amma in mutum ba shi da halin yin haka akwai wasu dabbobi da Allah ya halasta yin layya da su, kamar Tunkiya, Bunsuru Rakuma da Shanu, amma an fi karfafa yin layya da Raguna. Ya kuma kara da cewa, Allah Madaukakin Sarki ba Yana dubi ga girmar dabba ko tsadarta bane amma Yana dubi ne ga zuciyar mai layyar, saboda haka yakamata Musulmi ya yi aikin ibadar daidai karfinsa, ”Sai kaga mutum yana tunkarar Ragunan dubu dari ko abin da ya fi haka, bayan akwai raguna daidai karfinsa irin na dubu arba’in zuwa talatin’ in ji shi.
Malam Lukman Alfa ya kuma ce, an sunnanta raba naman layya kashi biyu zuwa uku, a raba wa ‘yan uwa da makwabta a kuma ciyar da iyali sauran, ta haka wadanda basu samu yin layyar ba za su amfana da naman. Daga nan ya nemi gwamnati ta kara kokari a kan kawo karshe matsalar tsaron da ake fuskanta a sassan kasar nan wanda yana daga cikin abubuwan da suka jawo tsadar dabbobi a wanan shekarar.