Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta yi aiki kafada da kafada da majalisa wajen kirkiran ayyukan sarakunan gargajiya a cikin kundin tsarin mulkin Nijeriya.
Tinubu ya bayyana hakan ne a wurin taron murnar cikar sarkin Ondo, Oba Bictor Kiladejo, shekara 70 da haihuwa, wanda ya gudana a garin Ondo.
- Na Gaji Mummunan Bashi Daga Gwamnatin Buhari – Tinubu
- Sakamakon Taron Kasashen Musulmi Da Larabawa: Saudiyya Da Nijeriya Za Su Jagoranci ‘Yantar Da Falasdin
Shugaban kasan wanda ya samu wakilcin ministan harkokin cikin gida, Hon. Olubunmi Tunji-Ojo ya tabbatar da cewa sarakuna na taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya a cikin gwamnatinsa wanda ake samun bunkasan al’adu a Nijeriya.
A nasa bangaren, Oba Kiladejo wanda ya gode wa Tinubu bisa halartar bikin ranar haihuwarsa na shekara 70, sannan kuma shekara 17 a kan karagar sarauta. Ya kuma ya ba wa shugaban kasan bisa nada Tunji-Ojo a matsayin minista.