Mataimakin shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya ce, daga cikin muhimman abubuwan da Nijeriya ke tunkaho da su a bangaren fasaha, masanaantun fitar da kayayyaki da kuma bangaren makamashi za su ci gaba da karfafa guiwa wa sashin zuba jari a yunkurin kyautata makamashi da kuma manufar kawo gagarumin sauyi ga tattalin arziki.
Ya shaida hakan ne a ranar Litinin yayin da ministan hadin kai don cigaba da tsarin sauyin yanayi na duniya na kasar Denmark, Dan Jorgensen, da ya kawo masa ziyara a fadar shugaban kasa.
- Man Da Nijeriya Ke Hakowa Ya Karu Zuwa Ganga Miliyan 1.35
- Kura-kuran Da Aka Tafka A Zaben Gwamna A Kogi, Imo Da Bayelsa
Da ya ke karin haske kan yunkurin da gwamnatin Bola Tinubu ke yi kan sauyin yanayi, Shettima ya ce, zuba jari a bangaren fasaha da makamashi hadi da sauran bangarori sun kasance masu fifiko a gwamnatin ne biyo bayan raguwar tattalin arzikin mai ke kawowa.
Shettima ya ce, Muna fuskantar kalubale amma muna kan kokarin shawo kansu. Shugaban kasa mutum ne wanda ke da zimma da kwazo da fikiran da zai jangoranci kawo gagarumin sauyi wajen ci gaban kasa. Harkokin Mai a tsawon shekaru ya kasance babban hanyar jagorantar tattalin arziki, amma a yan shekaru masu zuwa na fukantar tangarda.
Wannan dalilin ne ya sanya muka yi tunanin nemo mafita. A bisa haka, mun duba bangaren zuba jari a bangaren fasaha da makamashi hadi da sauran bangarori. Muna da damarmaki sosai da hadin guiwa da aiki tare za su taimaka mana. Kan hakan, ya nemi hadin guiwa da aiki tare da gwamnatin kasar Danish da cibiyar dadaitawa ta Afrika (GCAA) da shirin kula da sauyin yanayi na Nijeriya (NCA), mataimakin shugaban, ya ce, muddin bangaren makamashi ya samu kafuwa yadda ya dace, alummar Afrika za su samu cimma burin mafarkinsu a bangaren ci gaba mai ma’ana.
Ina rokon goyon bayanku da gudunmawarku domin ceto nahiyar Afrika, ya kara da cewa, inda ya nuna cewa Nijeriya tamkar ita ce jagaban ci gaban Afrika.
Mataimakin Tinubun, ya jinjina wa Denmark bisa jagorantar tsarin sauyin yanayi na duniya, sai ya nemi su dafa wa Nijeriya domin ta cimma gagarumin nasara a wannan bangaren.