Masu sanaar kiwon kifi a Nijeriya, na ci gaba da samun matsaloli ta fuskar koma baya tare da durkushewa a wannan sanaa tasu. Akwai manya-manyan dalilai da suke taka muhimmiyar rawa wajen durkushewar masu wannan sanaa a Nijeriya.
-Rashin Samun Kasuwa: Masu sanaar kiwon Kifi na fara wa ne da neman kasuwar da za su sayar da Kifin da suka kiwata, domin matsalar ita ce, a yayin da suke ci gaba da ciyar da su, Kwamin da suke kiwata su na adadin da zai iya dauka na yawan kifayen, ba sa wani kara ci gaba da yin girma.
- ‘Yansanda Sun Cafke Malamin Addini Da Sassan Mutum Danye A Oyo
- Wannan Kyauta Ce Ta Musamman Daga Daliban Makarantar Sakandaren Amurka
-Haka zalika, zabo gidan gonar da babu wadataccen ruwan da za a rika shayar da su, rashin kasa mai inganci da za a kafa kwamin kiwon Kifin da sauransu, na da matukar amfani wajen yin laakari.
-Sannan, gina kwami na siminti maras inganci wanda zai iya hujewa da rashin ba shi kuwalwar da ta dace, ba karamar matsala ba ce. Akwai kuma rashin daukar kwararrun maaiktan da za su rinka kwashe kifayen zuwa wani kwamin daban da sauran makamantansu.
-Sai kuma batun rashin tsara sanya hannun jari, wanda mafi yawan masu yin kiwon na tunanin kafin shiga cikin sanaar, sai sun tanadi kwamin kiwon masu yawa, wanda hakan ke sanya su kafa kwami masu yawan gaske a lokaci guda, inda hakan ke sanya wasu shafe tsawon lokaci ba tare da sun fara yin kiwon ba.
-Haka nan rashin sanin ilimin yin kiwon, domin kuwa ana son duk wanda zai fara sanaar ya kasance ya samu ilimin shiga sanaar kafin ya fara aiwatar da ita.
-Rashin daukar maaikatan da ba su dace ba, shi ma na matukar taimakawa wajen durkushewar wannan sanaa. Dalili kuwa, wadansu na daukar yanuwansu wadanda ba su da ilimi a wannan fanni a matsayin maaikatansu, inda hakan ke zame masu wani nauyi, sannan su gaza sallamar su daga wannan aiki, koda kuwa ba sa yi musu aikin yadda ya kamata ba.
-Har wa yau, rashin zuwan manajoji masu lura da gidan gonar, shi ma ba karamar matsala ba ce, domin kuwa kiwon Kifayen daga nesa ko kuma ta hanyar buga waya, domin bayar da umarni ga maaikata, ko shakka babu zai iya shafar tafiyar da gidan gonar.
-Rashin ciyar da su abincinsu yadda ya dace, shi ma na kawo nakasu ga wannan sanaa kai tsaye. Domin kuwa, rashin ilimi a kan abincin da zai rika gina wa Kifayen jiki, matsala ce mai zaman kanta. Dalili kuwa, da yawa daga cikin masu kiwon na sayen abincin ne mai rahusa, domin rage kashe kudade masu yawa. Bugu da kari, wasu masu kiwon ba sa lura da irin yanayin da kifayen nasu ke ciki tare da yanayin sauyin da suka samu, domin ba a cin kifi da ba shi da lafiya
-Gazawar daukar maaikatan da suka dace, don ciyar da kifayen tare da lura da yadda yanayin girman kifayen yake lokaci zuwa lokaci.
-Sai kuma batun rashin sanin yadda za a bai wa kifayen lulawa, ta yadda wasu masu gidan gonar kiwon kifayen, ba sa daukar maaikatan da suka dace; wadanda za su rika kula musu da kifayen yadda ya kamata.
-Mayar da hankali a kan kifaye yan kadan da ake kiwatawa, mai makon kifayen baki-daya, wannan ma wata babbar nakasu ce ga masu sanaar.
-Sannan, rashin adana bayanai da kuma rashin tantance kokarin da ake yi a kan kiwon, kan sanya su gaza sanin adadin ribar da suke samu ko kuma asarar da suka yi.
-Yin Kiwo a masayin shaawa, na sanya wa masu kiwon gaza kwashe kifayen da suka riga suka kammala girma a kan lokaci, inda suke ganin kamar suna kiwata manyan dabbobi ne a babban Kogi.
-Rashin Kwakkwarar manufa ta yin kiwon, ita ma na taka muhimmiyar rawa wajen durkushewar masu yin wannan sanaa, domin kuwa wasu na shiga cikin harkar ne kawai, domin ganin wasu abokansu na yi ko kuma burin samun wani tallafi daga wurin gwamnati.
-Akwai kuma batun sake fadada giraman kiwon kifayen, sakamakon rashin samun riba mai yawa da kuma rashin samun kifaye masu yawa. Wannan ba kasuwanci ne mai kyau ba, domin kuwa abin da ya fi dacewa shi ne, lalubo da mafita a kan matsalar da ta sanya mai sanaar kiwon ke gazawa, don yin gyara a kansu.
-Abu na karshe shi ne, yin ammana da rahotannin da jaridu da masu tuntuba suka wallafa na cewa, ana bukatar kudade yan kadan ne kawai a matsayin jari, a samu kazamar riba.