Shugaban Kungiyar Kwadago na Kasa (NLC), Kwamared Joe Ajaero, ya labarto yadda ta kaya da shi a lokacin da ya tsinci kansa a hannun ‘yansanda da kuma ‘yan daba yayin da aka masa biji-biji sa’ilin da suka shirya zanga-zanga a Jihar Imo.
Ajaero, wanda ke bayanin abun da ya faru a ganawarsa da ‘yan jarida a Abuja, ya ce, jami’an ‘yansandan da ke karkashin Jihar Imo ne suka kama shi, suka masa dukan tsiya, suka nemi makantar da shi tare da jan sa a kasa kamar dan ta’adda.
- Ribadu Ya Bukaci NLC Ta Janye Yajin Aiki, Ya Yi Allah Wadai Da Cin Zarafin Da Aka Yi Wa Ajaero
- Ba Ni Da Sha’awar Buga Wa Nijeriya Kwallo A Nan Gaba – Omorodion
Shugaban kwadago ya kuma karyata jita-jitan da ke yawo na cewa zanga-zangar da suka shirya yi a jihar ta siyasa ce. Ya ce zanga-zangar ta shafi yaki da rashin adalci da ake yi wa ma’aikata da kuma take musu hakki Jihar Imo.
Ya ce rashin jituwar da ake samu tsakanin kungiyar NLC da gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma na faruwa ne tun ma kafin ya zama shugaban NLC na kasa, don haka matsala ce wacce ta jima.
Ajaero ya ce NLC ba za taba ja da baya ba har sai lokacin da ma’aikata suka samu cikakken ‘yanci da walwala da kuma hakkokinsu.
Ya ce, “Jami’an ‘yansanda ne suka cafke ni suka duke ni da abubuwa daban-daban, inda suka tambayata mene ne ya sa nake kalubalantar gwamnan.
“Su wadannan mutanen su ne kuma suka dauke ni zuwa shalkwatar ‘yansanda domin magana da ogansu, sun tsaya a waje kamar suna jiran wani kasurgumin dan ta’adda.
“A wajen, na rokesu kan cewa ina bukatar na sha wasu magunguna, amma suka yi ta tuhumata na tsawon awanni. Ina tunanin a wannan gabar ne suka kai ni zuwa ofishin kwamishinan ‘yansanda. Shi kuma ya umarcesu da su kaini asibitin ‘yansanda,” ya labarto.
A gefe daya kuma, babban sufeto ‘yansandan, Kayode Egbetokun, ya umarci a gudanar da bincike dangane da abubuwan da suka wakana.