Hausawa na wa Sallah kirari da Sallah biki daya rana. A yanzu haka duk duniya ta dau harama ta gudanar da bukukuwan babbar sallar bana.
Mu ma a shafin Taskita ba a bar mu a baya, mun bi masu bibiyar shafin domin jin ko wanne irin Tanadi matasa suka yi wa wannan sallah?, Ko ta ya suke sarrafa naman layyarsu? Ga dai ra’ayoyinsu kamar haka:
Maryam Alhassan Dan-iya (Maryam Obam) daga Jihar Kaduna:
Eh na yi tanadi kala-kala kamar ta fannin girke-girke da nake son yi da kuma irin Kwalliyan da zan yi.
Eh! nan tunanin zani yawon sallah saboda wannan sallah din na layya ne zan zauna a gida in yi suya in na gama in ci in yi bacci, Sannan kwalliya zan yi amma ba sosai ba tun da wannan sallah aiki ya fi yawa.
Da farko idan aka datsa rago zan saka a tukunya in tafasa amma ba zan wanke ba dan Zakin naman zai ragu, in saka su kayan kamshi, albasa, thyme, garlic, albasa, da sauransu, in ya tafasu sai suya in mutum yana da barkono zai iya sakawa a naman bayan ya soya.
Na tanadan ma mai gida abubuwa kamar kwalliyan da zan masa abinci da abun sha kala biyu na gida dana waje Shawara shi ne ayi bikin sallah cikin kwanciyan hankali komai mai gida ya kawo a amsa ayi hakuri da shi.
Aliyu Idris Jihar Jigawa (Sarki Yakin Malumman Matazu):
Alhamdulillahi muna kara yi wa Allah godiya mai kowa mai komai, wanda a cikin Ikonsa ne ya kawo mu wannan babbar rana ta Babbar sallah mai tarin albarka.
Ni dai babban tanadi na nan shi ne na samu kaiwa iyayena, ‘yan’uwana, yayyu da sauran abokan arziki ziyara ta musamman domin mu gaisa da su mu sada zumunta.
Ina matukar nuna jin dadi na a ko da yaushe da zuwan wannan Babbar rana mai tarin albarka ta Sallah, kuma wannan rana abar alfahari ce ga kowa da kowa. Ni ma ina son na yi kwalliyata ta musamman mai kyau kamar yadda addininmu ya tanada, domin mu je mu yi Sallah da yi wa kasar mu addu’ar samun zaman lafiya. Sannan kuma akwai ziyara ta musamman zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki domin a sada zumunci.
A na iya gyaran Nama ta fuskoki da dama bayan idan an gama fede Saniya, Ragumi, Tunkiya da kuma d’an Akuya, duk ana iya gyarawa ta hanyar yi masa soya da Mai.
Babban abin da na tanadawa budurwata shi ne na ba ta barka da Sallah, da kuma kai ta zuwan gidan ‘yan uwana domin su sada zumunta.
Shawarata ga matasa a ko da yaushe su zama masu son zaman lafiya, kowa ya yi shagulgulan Sallarsa cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali, da kuma nuna halin d’a a ga iyaye da son zaman lafiya da junanmu a har kullum.
Ummi Isah Abubakar T/Wada:
Mun yi sabbin kaya duk dan bikin wannan babbar sallah, Kwalliyar Jalal bab zamu yi wannan sallah me riga, wannan na musamman ne ina son bashi ‘suprise’ ne bana son kowa ya sani, ina bawa samari shawara da mu ji tsoron Allah mu guje saka kan mu cikin mugayen ayyuka daga karshe ina yi mana fatan mu yi sallah lafiya.
Mansur Usman Sufi Sarkin Marubutan Yaki daga Jihar Kano:
Tanadin da na yi wa babbar Sallah shi ne zan kai ziyara da dukkan ‘yan uwana na jini da abokan arziki in sha Allah.
Kwalliyar da zan yi ita ce zan sanya manyan kaya da hula hade da takalmi, zan je duk wani guri da Allah ya bani iko. Da farko ana so kafin a sarrafa nama a tabbatar an tsaftace shi da abubuwan da za a sarrafa sa, a sulala shi sosai a sanya albasa da magi sannan a tsame sa, a zuba mai a kasko sannan a shiga soya sa. Bani da budurwa, amma na tanadar wa kanne na barka da Sallah.
Shawara ta dukkan Musulmi, da farko su zauna lafiya a taimaka wa wanda bai yi layya ba da nama cikin aminci ba tare da tozarci ba, mu kula da mutanen da za mu hadu da su a wajen ziyara domin tabbatar da lafiya su. Mu kai rahoto ga hukuma na abin da ba su aminta da shi ba.
Sunana Sadik Ashiru Abubakar Kano:
Na yi wa mata tanadi kamar yadda muka saba da Al’ada, na yi kayan sallah farare zan saka su in sha Allah, na tanadi turare da sauran abubuwa dai haka.
Gaskiya kwalliyar ‘yan birni zan yi wanda duk wanda ya ga kwlliyar sai ya yaba. Eh! to guraren da zan je; zan je gaishe-gaishe da gurin da ba a rasa ba. Yadda ake sarrafa nama ba a wanke shi a haka ake soyashi. Babu abin da na tanada domin ban da budurwar ma. Shawara ta ita ce ayi sallah lafiya, a gama lafiya, a kula da yara yadda ya kamata ban da cin nama sosai. Akwai ‘shoprite’ waje ne wanda ake yin bikin sallah wanda kowa da kowa yake zuwa ana more rayuwa.
Rukayya Ibrahim Lawal Sokoto:
Ni dai a bangare na har zuwa yanzu dai ban tanadar wa bikin sallah komai ba face shirin wasa hakorana don cin nama idan mai duka ya nuna mana.
Wannan sallar kamar yadda kowa ya sani ba sallah ce ta yawan kawa da yawace-yawace ba, sallar yin aiki ce tukuru don gyara tumbi. Akwai tanadin da na yi masa idan mai duka ya cika mini burina, amma abin sirri ne.
Shawarata ga matasa shi ne su gudanar da bikin sallar su a cikin tsanaki da kwanciyar hankali kamar yadda aka saba, sa’annan idan an zo shagalin cin nama a dinga sara ana duba bakin gatari saboda abin da ka iya zuwa ya dawo.