Dan kwallon Manchester United, Marcus Rahford, ya ce ya koma kan ganiyarsa bayan hutu da ya yi, sakamakon kammala kakar da ta wuce, kuma ya kara da cewar zuwan sabon kociyan kungiyar, Erik ten Hag ya zaburar da ’yan wasa, domin fuskantar kakar da za a fara a cikin watan Agusta.
Manchester United ta samu maki mafi muni a tarihin da take buga Premier League a kakar da ta wuce, inda magoya baya suka zargi Rashford, wanda ya ci kwallo biyar da rashin tagazawa a kakar wasan.
Sai dai shi kansa dan wasan ya fuskanci kakar wasa mafi muni da bai sa kwazo ba kamar yadda ya kamata a tarihin buga Premier League da ya ke yi, sannan dan kwallon tawagar Ingilan ya ce wannan hutun da ya yi ya kara samun kuzari, yana fatan haka sauran abokanan wasansa suke ji.
Kungiyar Manchester United za ta buga wasannin atisayen tunkarar kakar da za a fara a bana, inda za ta ziyarci Bangkok da Thailand da Melbourne da Australia da kuma Perth, haka nan kungiyar za ta ziyarci Oslo da Norway, sannan ta karkare da wasan sada zumunta a Old Trafford, domin magoya baya su shaida shirye-shiryen da ta yi.