Barkanmu da wannan lokaci barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai albarka, Wannan makon mun ji ra’ayoyin kune a kan tsadar ragunan layya a wannan shekarar, shin menene ya kawo haka.
Kamal Y. Iyantama
Hauhawar tashin Dala, yayin da Naira ke kara faduwa a kullum, kuma an kasa bin hanyar saukaka hakan bare a yi tunanin gyarawa. Wannan hakki ya fi yawa a kan hukumomi zuwa wadanda abin ya shafa.
Allah ya kyauta !
Shamsi Umar Bakanike Dambatta
Ni dai anawa ganin ba komai bane ya kawo wannan tsada illa rashin kudi a hannun al’umma domin kuwa rashin kudi shi kesa ake ganin tsadar abu da fatan dai Allah (S.W.T) ya hurewa al’umma, don ni wallahi ko kaza ban siya ba gashi lokacin yana kara gabatowa.
Aliyu Hassan Kumo
Akwai dalilai da dama wadanda suka sanya tsadar farashin, duba da yanayin kunci na rayuwa da kuma karancin kayan masarufi a sassa daban-daban.
Amma shi tsadar farashin Ragunan Layya yana da nasaba da yanayin da kasuwan take kai ne, akwai lokacin da za su iya sauka a lokaci daya, tunda dai da sauran lokaci kafin Sallah.
Kabiru Ado Muhd
Rashin tsaro da yawan hare-haren ta’addanci ke haifar da tsadar kayayyaki
Sadeek Rufa’i Ɗanguguwa
To ni dai a iya nazarina abinda ya kawo tsadar Dabbobi a wannan Shekarar a Nijeriya shine:
SHANU: A bana Shanu sun yi tsada sosai sakamakon tsadar abinci, da matsin tattalin arkirin wannan kasa, wanda ya katse batun tafiya aikin Hajji ga duk wanda suka biya a bana wanda ya taimaka wajen kawo tsadar Dabbobi kwarai da gaske.
Abinda mutane basu fahimta ba shi ne su masu kiwo sukan fidda Dabbobi ne su sayar lokacin da suke bukatar samun kudaden domin biyan bukatar su. To dukkanin lokacin tafiya aikin Hajji masu kiwo daga Kamaru, Chadi da Nijeriya sukan fidda Shanu domin tafiya aikin Hajji wanda a kan samu Shanu da yawa sun cika kasuwa to wannan shekarar babu aikin zuwa Haji ga wanda ya biya wannan shekarar din, don haka babu bukatar fidda Shanu masu yawa a sayar shi ne yasa Shanun suka yi karanci sosai wannan ya haifar da tsadarsu.
Wannan karanci ya sanya Shanu sun ninka kudin su kusan Kashi 1½ wannan shi ne ainihin abinda ya janyo matsalar tsadar su a wannan lokaci. Wanda zaka ga wai har da Sa kwara daya 2.5M a bana.
RAGUNA: A bana suma sun yi karanci kwarai da gaske, kuma abincinsu ya yi tsada, mafi yawanci ana samar masu da abinci ne daga masu noman rani da na damuna daga abinda suka noma, to amman a wannan shekarar taki buhu daya ya kai dubu 30 kenan ya ninka kudinsa a shekarun baya sau uku. Wanda hakan tasa manoma da yawa suka kasa noma wa dabbobi abinda za su ci, don haka an samu karancin lura daga makiyaya, sakamakon kkarancin abincin, wannan tasa dole duk wanda ya lura da Ragonsa yadda ya kamata ya bukaci kudi masu auki, wanda hakan ke sawa mutane suke kallon kamar Dabbobin sun yi tsada ne.
Muhd Basheer Sa’ad
Tsadar kayan abinchi shi ya kawo hakan, tunda suma dabbobin abinci ake basu kuma abincin nan saya ake da kudi wannan shi ne dalili
Aisha Muazu
Maganar gaskiya komai ya yi tsada, dusa da duk wani abu da ya shafi kiwo ya yi tsada. Yakamata mu fahimci wannan tsadar rayuwar ba mu kadai ya shafa ba a kasar nan, Mafi akasari ko’ina a fadin kasar nan ana fama da tsadar rayuwa. Mu dai yi fatan Allah kawo mana sauki a al’amuranmu, Allah ya hore mana yadda zamu yi mu rufa wa kanmu asiri. Mai Hali ya sayi ragon layya kuma kar ya manta da makobta da yan’uwa, wanda bashi da dama ya yi hakuri, Allah saukaka mana da karfin ikonSa
Hibburrasul Na Sidi Gusau
Lallai wannan magana haka take, Allah ka bamu abinda zamu yi layya dashi
El Rufai
Kinsan ragunan da dollar ake Sayo su, kuma tayi tsada
Omar Naseer Imam
Toh bana kam ba’a cewa komai kawai dai Alhamdulillah
Nuruddeen Musa Indabawa
tsadar abincinsu da wahalar kiwonsu, sai kuma tsabar son kudin wasu da magunta da rashin tausayi, a gefe guda kuma ana fama da rashi albashi a wasu jihohin kamar Kano da sauransu
kasuwanni sunui jugum jugum
U-Darasip Sunusi
Zamanin da aka nufata hakan dai faru ne ya zo
Junaed Badamasi Abdul Khadir
Rashin samun shugabanci nagartacce da rashin kauna da kishin junanmu