A yau Juma’a shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murnar bude taron kasa da kasa na karawa juna sani game da nazarin batutuwan da suka shafi kasar Sin ko “Shanghai Forum”.
Cikin sakon nasa, shugaba Xi ya ce wayewar kan kasar Sin ya kyautata, ya kuma bunkasa ta hanyar musaya, da koyi da juna tare da salon wayewar kai na sauran kasashen duniya, wanda hakan ya baiwa turbar wayewar kan Sin ginshiki mai zurfi.
- Kasashen Da Ke Kwashe Likitocin Nijeriya Za Su Fara Biyan Diyya – Ministan Lafiya
- Kasar Sin Na Gayyatar ‘Yan Kasuwa Daga Fadin Duniya Don Su Zuba Jari Da Ma Cin Gajiyar Nasarorin Da Ta Samu
Kaza lika, Xi ya ce yana fatan kwararru da masana daga sassan kasa da kasa za su kasance jakadun dunkule wayewar kan Sin da na sauran kasashen ketare, kana za su ingiza hade dukkanin sassa, da aiwatar da matakai a bude, tare da ci gaba da yayata bincike kan batutuwan da suka shafi kasar Sin, da musayar al’adu da koyi da juna.
Taken taron da aka bude a yau a birnin Shanghai shi ne “Wayewar kan Sin da turbar kasar a mahangar kasa da kasa”, yana kuma gudana ne bisa jagorancin hadin gwiwa tsakanin ofishin watsa labarai na majalissar gudanarwar kasar Sin da gwamnatin birnin Shanghai. (Mai Fassarawa: Saminu Alhassan)