Yayin da shugaban kasar Uruguay Luis Alberto Lacalle ya yi hira da wakilin babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG a kwanakin baya, ya yi nuni da cewa, bisa shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya, kasar Uruguay tana daya daga cikin manyan kasashen dake da hadin gwiwa mafi kyau da kasar Sin, domin kasar Uruguay tana da fifiko a bangaren mazauninta da yawan al’umma.
Shugaba Lacalle ya bayyana cewa, kasar Sin tana son tabbatar da ingancin kayayyaki da abinci, yayin da kasar Uruguay ke iya samar da kayayyaki masu inganci kuma ba tare da gurbata muhalli ba. Ya ce kayayyakin da kasar Uruguay ke fitarwa zuwa kasar Sin suna biyan bukatun kasar Sin, kana kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa zuwa kasar Uruguay su ma suna biya bukatun kasar Uruguay.
Ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin ta yi kokarin raya shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya, kuma kasar Uruguay tana fatan za ta kara samun damar hadin gwiwa da kasar Sin karkashin shawarar. (Zainab)