Tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai kuma dan majalisa mai wakiltar mazabar Tudun Wada/Doguwa na Jihar Kano, Alhassan Ado Doguwa, ya yi ikirarin cewa jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar ta lashe zaben 2023 ta hanyar magudi.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa jam’iyyar NNPP ta samu rinjayen kuri’u a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 da kuma kujeru masu rinjaye a zabukan ‘yan majalisar dokokin jihar da aka gudanar a rana guda.
- Barcelona Ta Tsallaka Mataki Na Falan Daya Bayan Doke Porto
- Basirar Kasar Sin Na Iya Saita Alkiblar Warware Rikicin Palasdinu Da Isra’ila
Daga nan ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ayyana jam’iyyar a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Sai dai kotun sauraren kararrakin zabe ta jihar ta rushe nasarar da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya samu a watan Satumba, inda a maimakon haka ta ayyana dan takarar jam’iyyar APC, Nasir Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
NNPP ta garzaya kotun daukaka kara, wadda ita ma ta tabbatar da hukuncin da kotun ta yanke a kan Gawuna da APC, lamarin da ya jefa Jihar Kano cikin rudani.
Da yake mayar da martani a shirin talabijin na Channels a ranar Laraba, Doguwa, wanea jigo be a jam’iyyar APC ya ce kotu kawai ta fallasa magudin zabe sa NNPP ta yi a zaben 2023.
Ya ce an ayyana jam’iyyar ce ta lashe mafi yawan zabukan “saboda sun samu damar yin katin zabe ba bisa ka’ida ba.
Sai dai Doguwa bai yi karin haske kan yadda jam’iyyar NNPP ta samu katin zabe ba bisa ka’ida ba a lokacin zaben.