Saura wata daya ke nan za a kawo karshen wannan shekarar da ya yiwu ta kasance mafi zafi a tarihin dan Adam, kuma a daidai wannan lokaci, aka kaddamar da taron bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD karo na 28(COP28) a birnin Dubai na hadaddiyar daular Larabawa.
Sai dai kuma a yankin Kahon Afrika, kasashen Kenya da Habasha da Somaliya na fuskantar ambaliyar da yanayin da ake kira Elnino ke haifarwa, biyo bayan mummunan bala’in fari da ba a taba ganin irinsa ba cikin shekaru 40 da suka wuce, da ya afka musu ba da jimawa ba.
- Labarin Zamanintarwa Irin Na Kasar Sin: Kimiyya Na Taimakawa Manoma Fita Daga Kangin Talauci
- Ya Kamata The British Museum Ta Mayar Da Kayayyakin Al’adu Da Aka Sace
Nazarin da aka gudanar ya shaida cewa, irin munanan yanayin da aka fuskanta a yankin kahon Afirka na da alaka da matsalar sauyin yanayi da ayyukan dan Adam suka haifar. Don haka ma, shugaban kasar Kenya William Ruto a yayin ziyarar da ya kai Turai a kwanan baya, ya yi gargadin cewa, Afirka na kara fuskantar matsalar yanayi.
Abin haka yake, sabo da abin da ya faru a yankin kahon Afirka yana kuma faruwa a sauran sassan nahiyar Afirka. Idan ba a manta ba, a bara, ambaliya da ta afkawa Nijeriya ta kasance mafi muni ga kasar cikin shekaru 10 da suka wuce, wadda ta halaka sama da mutane 600, tare da raba wasu miliyan 1.3 da muhallansu, baya ga yadda ta lalata gidaje kimanin dubu 82 da ma gonaki masu fadin eka dubu 110.
To, a irin wannan halin da ake ciki na kara samun zafin yanayi da ma bala’u daga indallahi, kasa da kasa ma na kara fahimtar muhimmancin daukar matakai na tinkarar sauyin yanayi. Taron COP28 da ke gudana a Dubai ya samu halartar mutane sama da dubu 70, abin da ya sa ya kasance mafi kasaita a tarihin taron, wanda ya shaida yadda kasa da kasa suke dora muhimmanci a kan batun tinkarar sauyin yanayi.
Kasar da ke karbar bakuncin taron ta kasance kasa ta biyar a duniya wajen yawan samar da man fetur, duk da haka, kasar na ganin dole ne a sauya fasalin makamashin da ake amfani da su.A yankin hamadar da ke kusa da birnin Abu Dhabi, babban birnin kasar, akwai wata tashar samar da wuta da makamashin rana da ta kasance irinta mafi girma a duniya, wadda wani kamfanin kasar Sin ya dauki nauyin gina ta, tashar da ake kira Al Dhafra. An ce, tashar na iya biyan bukatun magidanta kimanin dubu 200, wadda kuma za ta rage iskar Carbon da ake fitarwa da kimanin ton miliyan 2.4, kwatankwacin yawan iskar Carbon da motoci dubu 500 ke fitarwa.
Sai dai ba wani abin mamaki ba ne yadda kamfanin kasar Sin ya samar da wannan tasha da ta kasance irinta mafi girma a duniya, sakamakon yadda kullum kasar Sin ke dora matukar muhimmanci a kan kiyaye muhalli, wadda take daukar kwararan matakai na tinkarar matsalar sauyin yanayi.
A nan kasar, akwai tsarin samar da makamashi mai tsabta mafi girma a duniya, kuma kasar ta kasance kasar da iskarta ta fi saurin inganta da ma kasar da dazuzzukanta suka fi saurin karuwa cikin shekaru 20 da suka wuce.
A sa’i daya kuma, kasar Sin ta yi kokarin sa kaimi ga aikin daidaita matsalar sauyin yanayin duniya, wadda ta aiwatar da ayyukan irinsu tashar Al Dhafra a sassan duniya. Misali, a Afirka, tashar samar da wuta da makamashin rana ta Garissa, wadda kamfanin kasar Sin ne ya gina, ta kasance mafi girma a gabashin Afirka,kuma bayan da aka fara aiki da ita a shekarar 2019, tana samar da wuta sama da KW miliyan 76 a kowace shekara, wadda ke iya biyan bukatun mutane sama da dubu 380, wadda ta yi matukar saukaka matsalar karancin wutar lantarki da aka fuskanta a wurin.
Yanzu haka wakilan kasa da kasa na haduwa a wajen taron COP28 a Dubai, don gano bakin zaren warware matsalar sauyin yanayi da ke addabar dan Adam. Kasar Sin a nata bangaren, na fatan hada kai da bangarori daban daban, don samar da karin gudummawa da dabaru wajen daidaita matsalar sauyin yanayin duniya.