Rundunar ‘Yan sandan jihar Ondo ta cafke wata mata mai suna Misis Christiana Kehinde da laifin tsoma hannun jikarta cikin ruwan zafi a garin Ondo.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, Funmilayo Odunlami, ya ce wani makwabcin matar da abin ya shafa ya kai rahoto kan laifin cin zarafin yara da ake zargin matar.
- Arangama Da ‘Yan Bindiga: Mutum 12 Sun Sheka Barzahu
- Mun Cafke Wadanda Ake Zargi Da Kai Hari A Cocin Katolika Dake Ondo – Amotekun
Jami’in hulda da Jama’ar ya ce matar mai shekaru 52 ta tsoma hannun yarinyar a cikin ruwan zafi sannan ta barta a gidan saboda ta saci tukunyar miya, hannayen sun kusan konu kafin a kama matar.
Odunlami ya ce, “A ranar 6 ga watan Yuni, 2022, wani makwabcin da abin ya shafa ya ba da rahoton laifin cin zarafin yara kan wata Misis Christiana Kehinde mai shekara 52 mai lamba 13 Abejoye Odojoka, cikin garin Ondo.
Ta ci gaba da cewa, matar da ko da yaushe ta kasance mai son cin zarafin jikarta Suliat Tunde mai shekara 8, ta tsoma hannun yarinyar a cikin ruwan zafi ta ajiye ta a gidan saboda ta saci tukunyar miya da hannu kusan har sun kusan rubewa.
“An fara bincike ne yayin da wadda ake zargin ta yi ikirarin cewa tana kokarin yin amfani da hakan ne kawai a matsayin wani mataki na hana ta shanmiya ba tare da amincewarta ba.
“An mika yarinyar zuwa cibiyar Trauma da ke garin Ondo domin yi mata tiyata.”