Majalisar Zartaswar Gwamnatin Jihar Adamawa, ta amince da kasafin kudin naira miliyan dubu dari biyu da ashirin da biyar da miliyan dari takwas, (Naira 225.8m), a matsayin kasafin kudin shekarar 2024.
Kiyasin kasafin kudin da gwamnatin jihar za ta kashe, an sanar da shi ranar Alhamis bayan kammala zaman majalisar, da gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, ya jagoranta.
- Wang Yi: Sin Da Angola Sun Kafa Misali Na Hadin Gwiwar Kasashe Masu TasowaÂ
- Kisan Masu Mauludi A Kaduna Abun Takaici Ne – Bukola Saraki
Da yake yi wa manema labarai karin bayani a gidan gwamnatin jihar, kwamishinan yada labarai da tsare-tsare, Neido Geoffrey Kafulto, ya ce an kididdige adadin kudaden bisa la’akari da bukatun jama’ar jihar.
Shi ma a nasa bayanin, kwamishinan ma’aikatar kasafi da tsarawa Emmanuel Piridimso, ya ce an tsara za a maimaita kashe naira biliyan 111 da miliyan uku, kashi 43.3 bisa dari na kasafin kudin, sai kuma naira biliyan 114 da miliyan biyar, da yake kashi 50.7 bisa dari, za a kashe su kan manyan ayyuka.
Kwamishinan ya ce gwamnatin ta kammala shirin gabatar da kasafin gaban majalisar dokokin jihar a ranar Juma’a, domin neman sahalewar ta.