Tun ranar 7 ga watan Oktoba, tambayoyi da dama suke bijirowa a tsanake daga kafofin yada labaran Turawan Yamma iri daban-daban tare da yin amfani da su a matsayin gabatar da tattaunawa a gidajen talabijin dinsu da zimmar cewa, suna wakiltar masu kallo da sauraro. A wannan rubutu, zan kalubalanci daya daga cikin wadannan tambayoyi.
Bayan labari mai tsawo na abin da ya faru a safiyar ranar 7 ga watan Oktoba, ko shakka babu; labaran da aka kirkira aka kuma zuzuta su marasa dadi a kan Isra’ila, su ake ta sake maimaitawa, abin tambaya a nan shi ne, ko ka yi tir da wannan?
Babu shakka, dukkannin mu mun kalla a talabijin yadda mayakan Falastinawa suka mamaye iyakoki a 1967, sannan mun kwana da sanin yadda sojojin Isra’ila da dama suka mutu a wannan safiyar, haka nan yadda aka tasa keyar da dama daga cikin fararen hula na al’ummar Isra’ilan zuwa Gaza a matsayin fursunoni.
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Gina Asibiti, Makaranta Da Gidaje Ga Al’ummar Tudun Biri – Gwamnan Kaduna
- Sin: Ya Kamata Kwamitin Sulhu Ya Kara Daukar Matakai Kan Lokaci Don Inganta Tsagaita Bude Wuta Da Kawo Karshen Yaki A Dukkan Fannoni
Wannan bai kamata ya zama maudu’in da za a tattauna a kansa ba, in dai ba zancen kurame ake so mu yi ba. Don haka, da zarar an ga sun fara yin wannan tambayar tare da gabatarwa mai tsawo, to sun gama da kai, domin kuwa za a dauki hakan a matsayin wata babbar hujja. Sannan, za su nemi amsa ta kasance cikin dayan biyu, ko eh ko a’a. Wannan kai tsaye rashin adalci ne, dalili kuwa cewa eh ko a’a, yana nufin ka ware wannan rana kenan daga cikin kundin tarihin abin da ya faru.
A siyasa, musamman idan aka yi la’akari da abubuwan da suka faru tare da bayyana gaskiyar al’amarin abin day a wakana, muna bukatar isasshen fili domin tattauna wannan al’amari, idan kuma ba haka ba, za ta kai ga an tilasta mana daukan bangaranci, tun da ba mu da wani zabi. Idan kuma muka amince da cewa, wadannan yake-yake da wannan bala’i za a kawo karshensa ta bangarensu da kuma bangaren abin day a faru daga tarihi, ko shakka babu wannan zai bude hanyar kisan kare dangi.
Abin da ya faru a ranar 7 ga Oktoba ya riga ya faru, a cikin abubuwan da muke gani a shafukan sada zumunta da kididdigar da ake fitowa da ita, lallai akwai bukatar fito da abubuwa da dama da suke a boye tare da bayyana su kowa ya sani, daga nan gaskiyar za ta bayyana kuru-kuru. Sanin kowa ne, ba a bari al’umma su san sirrin da ke tattare da sojoji, tun da suna da salo da hanyoyin dabaru iri daban-daban wanda bas a so al’umma su sani.
Ranar 7 ga watan Oktoba na da matukar tushe a tarihi, shekara 106 da ta gabata, Kasar Birtaniya ta shuka mummunan iri na rashin gaskiya, cin zarafi da kuma zalinci ga al’ummar Falastin, wanda ya yi sanadiyyar wahalar da suke fama da ita har zuwa yanzu ta hanyar fitar da mummunan sanarwar Balfour a ranar 2 ga watan Nuwambar 1917, wanda a wancan lokacin; Kasar Birtaniyar ba ta san komai na tarihi game da Falastin din ba.
A sanarwar da Birtaniyar ta bayar, ta mallaka wa Yahudawan Turai su gina kasar a matsayi kasa, ba tare da yin la’akari da asalin masu kasar ba da kuma hakkin da suke da shi dokance.
Ba za mu taba raba ranar 7 ga watan Oktoba daga Al-Nakba(ranar bala’i) ba tare da irin hukuncin da muka fuskanta a shekara 1948, bayan shekara 10 cif da ‘yan ta’addan Yahudawa da suka hada da Lehi, Irgun, da kuma Haganah suka yi wa ‘yan’uwanmu kisan kiyashi.
Abin day a faru a Deir Yasin da Hotel din King Dabid da kuma Al Tantura da sauran makamantansu, ba za mu taba mantawa da shi ba har abada, wanda wannan kisan kiyashin da aka yi wa Falastinawa ne ya yi sanadiyyar mafi yawancinsu zama ‘yan gudun hijira a Kasashen Lebanon, Siriya, Jodan, West Bank da kuma Gaza.
A shekarar 1948, bakin haure sun samu cikakken daurin gindi tare da gudunmawa daga wurin Turawan Kasashen Yamma, na korar Falastinawa tare da gina kasar da kashi 78 cikin 100 na tarihinta tamu ce.
Ba za taba tunawa da ranar 7 ga watan Oktoba ba tare da tunawa da ranar 6 ga watan Yunin 1967 ba, yayin da Isra’ila ta samu nasarar sake mamaye kasha 22 cikin 100 na Kasar Falastin mai cike da tarihi. Tun wancan lokaci, kimanin shekara 56 kenan suna fama da wannan zalinci da rashin adalci da fifikon Yahudawa a kan Falastinawa.
Ranar 7 ga watan Oktoba, ta fallasa Kasashen Yammacin Turai da dama ta fuskar son zuciyar shugabaninsu da amfani da kafafen yada labaransu, babu kunya babu tsoron Allah suna goyon bayan kai hari na ta’addanci a kan mutanen da suke da hakki a kan kayansu, wanda wannan zalinci ne karara.
Saboda haka, idan muka yi nasarar magance wannan matsala tun daga tushe tare da daga‘yan yatsunmu a kan damuwar da muke ci gaba da ji, ranar 7 ga watan Oktoba za ta kasance ranar da dukkannin mu za mu farka daga dogon baccin da muka jima muna yi, ma’ana, muna share fagen zaman lafiya mai dorewa kenan.
Har ila yau, amsar tambayar Falastinawa ta dogara ne ga dokokin kasa da kasa, kudirin majalisar dinkin duniya 181, 194, 242,388 da kuma wasu da dama daga cikin kudirorin majalisar dinkin duniyar wadanda za su sanya Falastin kasancewa cikin tsarin kasa mai zaman kanta tare da yi wa Falastinawan adalci wajen dawo da ‘yan gudun hijira kamar yadda kudirin majalisar dinkin duniya na 194 ya tanadar, ita ce kawai hanyar da ta dace wajen tabbatar da cewa, babu wata ranar 7 ga Oktoba da za a sake yi maimaita kisan kiyashi.