Babban taron MDD ya ci gaba da gudanar da taron musamman na gaggawa, domin tattauna batutuwan da suka shafi zirin Gaza. Kuma a yayin zaman na jiya Jumma’a, wakilin kasar Sin ya yi maraba da kudurin tsagaita bude wuta da aka amince da shi a ranar Talata 12 ga watan nan, wanda ke kunshe da bukatar tsagaita bude wuta nan take a zirin Gaza bisa dalilai na jin kai, kana ya bukaci a aiwatar da dukkanin kudurin yadda ya kamata.
Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya ce kasarsa ta yi maraba da wannan kuduri, wanda ya samu amincewar akasarin kasashe mambobin majalisar, ya kuma dace da burin al’ummun kasa da kasa, don haka ya wajaba a aiwatar da shi yadda ya kamata. To sai dai kuma, mista Zhang ya ce kwamitin tsaron MDD ya gaza wajen aiwatar da ko da kira, na a tsagaita bude wuta.
- Ma’aunan Kasar Sin Na Gina Layin Dogo Da Aka Wallafa Da Yarukan Waje Sun Taimaka Wajen Raya Shawarar BRI
- Ina Fatan Allah Ya Dauki Rayuwata A Dakin Mijina -Tsohuwar Jaruma Fati Ladan
Zhang Jun ya jaddada cewa, Sin na matukar adawa, ta kuma yi tir da dukkanin wasu hare-haren da ake kaiwa fararen hula. A halin da ake ciki yanzu, tsagaita bude wuta ya kamata a fara aiwatarwa, kuma dole ne sassan kasa da kasa su mayar da wannan buri mafi muhimmanci da ake bukata cikin gaggawa.
A ranar Talata ne babban taron MDD ya gudanar da zaman gaggawa na musamman, inda ya zartas da kuduri bisa babban rinjaye, da goyon bayan kasashe 153, wanda ya yi kira da a dakatar da bude wuta bisa dalilai na jin kai a zirin Gaza, kana kudurin ya jaddada bukatar baiwa fararen hula kariya, bisa tanadin dokokin kasa da kasa, kana a gaggauta sakin wadanda ake tsare da su ba tare da gindaya wani sharadi ba.(Saminu Alhassan)