Manyan hafsoshin sojan Nijeriya 113 sun yi ritaya a wannan shekarar kamar yadda Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya bayyana, ministan ya yaba musu kan sadaukarwar da suka yi na tabbatar da zaman lafiyar Nijeriya.
Ministan ya kuma ba su tabbacin biyansu hakkokinsu na fansho cikin gaggawa.
- Muna Bukatar Gudunmawar Addu’o’in ‘Yan Nijeriya Don Yaki Da Matsalar Tsaro — Badaru
- Tsaro: Yadda Sojoji Ke Rakiyar Matafiya Tsakanin Gusau Zuwa Dansadau
Badaru ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Talata, 19 ga watan Disamba, 2023, a yayin wani taron cin abincin dare wanda aka shirya don karrama sabbin manyan hafsoshin da wadanda suka yi ritaya daga aikin soja da aka gudanar Asokoro, Abuja.
Wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ya ce wadanda aka karrama sun hada da Janar daya, Laftanar Janar daya, Manjo Janar 67 da Birgediya Janar 44.
Ministan ya bukaci wadanda suka yi ritayar da su yi tunanin yadda za su tunkari kalubale na gaba bayan barin su aiki, ya kuma ba su tabbacin kudirin Gwamnati na gaggauta biyan kudaden fansho na ma’aikatan da suka yi ritaya.