Uwargidan Shugaban Kasar Nijeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta raba Naira miliyan 25 ga mabukata 250 ta hanyar shirin Renewed Hope Initiative Elderly Support Scheme (RHIESS) a Jihar Kebbi.
Sanata Oluremi Tinubu ta samu wakilcin uwargidan gwamnan Kebbi, Hajiya Zainab Idris, wadda ita ce ko’odinetan shirin na jihar a babban bugu na RHIESS a Birnin Kebbi.
- Tinubu Ya Sake Bullo Da Shirin Ciyar Da Dalibai A Makarantu
- Kotun Ƙoli Ta Kammala Sauraron Ƙarar Zaɓen Kano, Za Ta Sanar Da Ranar Yanke Hukunci
Ta ce, “Wannan shirin ne na tallafa wa marasa galihu 250 ‘yan kasa da suke da shekaru 65 zuwa sama a fadin dukkan jahohin tarayya 36 hadi da babban birnin tarayya da kuma tsofaffi daga kungiyar matan jami’an tsaro na ‘yansanda (DEPOWA).
“Wadannan zababbun wadanda za su ci gajiyar shirin za su karbi kudi Naira 100,000 kowannensu, domin a rage musu radadin talaucin tabarbarewar tattalin arziki da kuma rage wa manyanmu da suke fama da bukata a rayuwasu.”
Matar Shugaban kasa, ta kara da cewa jimillar kudaden da aka fitar sun kai Naira miliyan 950 kamar yadda hukumar gudanarwar kungiyar Renewed Hope Initiative ta amince.
A cewarta, kowace jiha ta tarayya za ta karbi kudi har Naira miliyan 25 don tallafa wa mutanen jiharsu.
“Mun himmatu wajen ganin kowace jiha ta samu wannan tallafi, ba tare da nuna wariyaba,” in ji ta.
Misis Oluremi Tinubu, wadda ta jaddada muhimmancin ba da fifiko ga tsofaffi a cikin shirin, ta ce kula da su wani bangare ne na girmama su da gudunmawar da suka bayar tare da amincewa da haduwar da suka fuskanta.
Haka zalika ta ce “Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta ba da kulawa ga manyan ‘yan kasarmu, haka kuma za a ba da fifiko ga kiwon lafiyarku, ilimin yara kananan, don rage muku walhalhalu rayuwa.
A wani bangare na tallafin da jihar ke bai wa shirin, sakatariyar dindindin ta ma’aikatar harkokin mata da ci gaban jama’a ta jihar, Hajiya Aisha Maikurata, ta bayyana cewa gwamnatin jihar ta kaddamar da tallafin ba da kiwon lafiya a kyauta tare da raba kayan abinci iri-iri ga dattawan jihar.
“Ma’aikatarmu tana tallafa wa tsofaffi, gajiyayyu da masara galihu da kuma masu karamin karfi a kyauta tare da rarraba sauran kayayyaki ga wadanda suka amfana kamar yadda ya kamata, don tabbatar da nasarar wannan shirin,” in ji ta.
Hajiya Aisha Maikurata ta gode wa uwargidan shugaban kasa da gwamnatin jihar da kuma uwargidan gwamnan bisa kokarinsu na ganin an samu nasarar raba wa wadanda suka ci gajiyar tallafin.
Da yake mika godiyarsa ga uwargidan shugaban kasar, Alhaji Ahmad Mahmud, wanda ya yi magana a madadin wadanda suka ci gajiyar tallafin, ya bayar da tabbacin cewa za a yi amfani da wannan karimcin cikin adalci domin cimma burin da aka sa a gaba.