Shugaba Bola Tinubu, yayi Allah-wadai dangane da mummunan harin da ‘yan bindiga suka kai Jihar Filato wanda yayi sanadiyyar rasa rayuka da dukiyoyi.
Shugaban ya fadi hakan ne a cikin wata sanarwar manema labarai da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Talata.
- Tinubu Ga Gwamnoni: Dole Ne Mu Tabbatar Da Zaman Lafiya A Nijeriya
- NAF Ta Lalata Haramtattun Wuraren Tace Mai Guda 6 A Ribas
Shugaba Tinubu ya umarci jami’an tsaro da su dauki matakin gaggawa, tare da hada karfi da karfe domin zakulo duk wadanda suka aikata wannan mummunan hari da tabbatar da kamo masu hannu a ciki.
Shugaba Tinubu ya bayyana kakkausar suka dangane da munanan hare-haren da aka kai a kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi na jihar Filato, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 160,
Sai dai rundunar ‘yansandan Jihar Filato ta ce mutane 96 ne aka hallaka a hare-haren.
An kai hare-haren ne a daren jajierin ranar Kirsimeti 24 ga watan Disamba da kuma washegari ranar Kirsimeti, inda ‘yan bindiga suka mamaye kauyuka da dama a kananan hukumomin da abin ya shafa.
Baya ga mutane da suka rasa rayukansu, akwai kuma daruruwa wadanda suka jikkata wadanda ake kula da su a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos da kuma asibitin gwamnati da ke Barikin Ladi.