Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, ya yi watsi da rahoton da ke yawo na haramta sha da sayar da giya a jihar.Â
Bago ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Alhamis.
- Harin ‘Yan Bindiga: Shettima Ya Kai Ziyarar Jaje Jihar Filato
- An Masa Daurin Rai Da Rai Saboda Yin Fyade A Masallaci A Bauchi
Ya ce irin wannan umarnin ba shi ne ya ba da bayar ba ko kuma mataimakansa ba, ya kara da cewa ya kamata jama’a su yi watsi da rahoton da ke fitowa daga shafukan sada zumunta.
A cewarsa, an ja hankali ga wani rahoto da ya karade wasu shafukan da ke ikirarin cewa gwamnatin Jihar Neja, ta haramta sayar da barasa.
Ya kara da cewa an yi gwamnatinsa karya kan cewa ta hana sha da sayar da barasa a kananan hukumomi tara na jihar, ciki har da Suleja.
“Muna so mu bayyana cewa gwamnan, wanda ya shagaltu da tunkarar ayyukan jama’a da dama a fadin jihar, bai taba bayar da irin wannan umarnin ba.
“Har yanzu gwamna ba kafa hukumar ba da lamuni da ba da lasisi ba, don haka, babu wani umarni irin wannan da zai iya fitowa daga hukumar da ba a kafa ba.”
Sanarwar ta ce Bago ya umarci jami’an tsaro da su kama sakataren hukumar da aka nada mai suna Mohammed Ibrahim.
“Muna gayyatar jama’a nagari da abokanmu a kafafen yada labarai da su yi watsi da duk wani furuci.”
Ya ce ya kamata a gabatar da bincike ga jami’an da aka ba su izinin yin magana a madadin gwamnatin jihar.