Bangaren kiwon lafiya a Nijeriya ya dade yana bukatar a kawo mashi dauki, a ‘yan shekarun nan gwamanatin Nijeriya ba ta samar da isasasun kudade ba ga harkar kiwon lafiya a Nijeriya, gwamnati ta kasa cika alkawarin da ta dauka a taron kasashen Afirka da aka yi a Abuja na ware kashi 15 na kasafin kudin kasa ga bangaren kiwon lafiya.
Yana da matukar muhimmanci a gane cewa, kusan shekara biyu da suka wuce kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta yi wani gangamin yaki da wasu manyan cututtuka da suka addabi al’umma, cuttukan sun hada da cutar Kanjamau,Tarin Fuka, Maleriya da sauran cututtukan da za a iya kare al’umma daga kamuwa da su a nahiyar gaba daya.
- Hukumomin Sin Na Adawa Da Munanan Tanade-tanade Dake Da Alaka Da Sin A Cikin Dokar Ba Da Izinin Tsaron Amurka
- Jirgin Ruwa Mai Binciken Teku Na Farko Na Kasar Sin Ya Gwada Yin Aiki Cikin Nasara
A taron da ya gudana a ranar 27 ga watan Afrilu 2001, an yi alkawura da dama da suka hada da alkawarin da Nijeriya ta yi na ware kashi 15 na kasafin kudinta a duk shekara ga bangaren samar da cikakkiyar kula da lafiyar al’umma, kasashen sun kuma yi alkawarin samar da issasun kudade don bunkasa harkar samar da kiwon lafiya a fadin nahiyar Afirka gaba daya.
A wani rahoto da wata kungiya mai zaman kanta mai suna PACFaH @Scale ta wallafa inda ta yi nazarin kasafin kudin kasashen Afirka na tsawon shekara 10, ta gano cewa Nijeriya ta kasa cika alkawarin da ta yi na bayar da issasun kudi ga bangaren kiwon lafiya, inda a wasu lokutta ma kasafin kudin kiwon lafiya ba ya kaiwa kashi 3 a cikin kasafin kudin shekarar.
Wannan watsin da aka yi da bangaren kiwon lafiya ya sa bangaren ya yi tabarbarewar da ba a taba gani ba a tarihin kiwon lafiya a Afirka.
Idan za a iya tunawa, ministan lafiya na gwamnatin tsohon Shugaba Kasa Muhammadu Buhari, Olorunnimbe Mamora ya bayyana cewa, kashi 3 cikin dari na cibiyoyin kiwon lafiya 30,000 da ake da su a Nijeriya ne kawai ake tafiyarwa yadda ya kamata.
Sakamakon wannan barakar a bayyane yake cewa, ‘yan Nijeriya na kashe fiye da Dala biliyan 2 a duk shekara wajen neman lafiya a kasashen waje yayin da kuma a gida a ke fafatawa da cututtukan da za a iya kare al’umma daga kamuwa da su amma kuma sai ga shi suna zama sanadiyar mutuwar mutane da dama.
Sai dai kuma an samu kwarin gwiwa a wannan makon yayin da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya dauki wasu mihimman matakai na ware makudan kudade ga bangaren kiwon lafiya a Nijeriya.
A bikin ranar samar da lafiya ga al’ummar duniya, gwamnatin Bola Tinubu ta fito da wasu shirye-shirye da suka hada da gaggarumin zuba jari a bangaren kiwon lafiyar al’umma da kuma abin da ya shafi gine-ginen sabbin asibitoci da gyara wadanda ake dasu, haka nan kuma gwamnati ta bayar da tabbacin hakan zai dore na shekaru masu zuwa. Wannan ya kuma hada da alkawarin tabbatar da cibiyoyin samar da lafiya da dama a sassan kasar nan suna tafiya yadda ya kamata. Gwamnatin ta kuma shirya sake fasalin tsarin bayar da tallafin kiwon lafiya ga al’ummar Nijeriya don mutane da dama su amfana kamar yadda dokar samar da kiwon lafiya ta kasa ta tanada (National Health Act).
Wannan jaridar ta yi imanin cewa, ya kamata a ce tuntuni aka samar da wadannan dokoki amma duk da haka muna maraba da gabatar da su da aka yi a wannan lokacin.
Yanzu da aka dawo da martabar harkar kiwon lafiya, gwammnatin Tinubu na da damar samar da ingantaccen kiwon lafiya na dukkan al’ummar Nijeriya kamar yadda ake fata, ba wai ya zama tamkar irin bayanan da ‘yan siyasa ke yi ba don samun kuri’un al’umma.
Dole ne a yaba wa wannan gwamnatin a kan yadda ta tsara wa kanta abubuwan da take son cimmawa a nan gaba, wadanda suka hada da samar da karin biliyoyin nairori ga bangaren kiwon lafiya, da kuma samar da hanyoyin sa idon don ganin ana kashe kudaden kamar yadda ya kamata.
Sai dai kuma shi tsarin, samar da tsare-tsare masu kyau ga bangaren kiwon lafiya kawai ba zai isa ba har sai gwamnatin ta yi maganin matsaloli da tarnakin da bangaren lafiya a Nieriya yake fuskanta wadanda su ne suka kawo wa bangaren cikas a shekarun baya.
Ba za a amince da masu karkatar da kudaden da aka ware wa bangaren kiwon lafiya ba, ya kamata a samar da masu bincike akai-akai don ganin yadda ake kashe kudaden.
Idan har ana son tabbatar da canje-canjen da ake bukata, dole a samu hadin kai a tsakanin gwamnatocin tarayya da na jihohi, a kuma kawar da bambance-bambancen siyasa don samun cikakiyyar nasarar da ake bukata.
Dole gwamnonin jihohi su sauke nasu hakkokin da suka rataya a kansu, sun kuma hada da tabbatar da kiwon laifiya ya isa ga kowa, sayo magunguna da kuma horar da kananan ma’aikatan kiwon lafiya, domin gwamnatin tarayya ba zai yiwu ta sa hannunta a cikin komai ba.
Haka kuma bangaren masu zaman kansu na da muhimmiyar gudunmawar da za su iya bayarwa, wadanda suka hada da kafa kamfanonin harhada magunguna da kuma samar da magungunan rigakafin cututtukan kananan yara.
Tabbas ‘yan Nijeriya na da hakkin neman a samar masu da ingantaccen kiwon lafiya musamman ma ganin yadda bangaren ya tabarbare a ‘yan shekarun nan.Ya kamata kungiyoyi masu zaman kansu su dauki nauyin sa ido a kan yadda ake kashe kudaden da aka ware wa bangaren lafiya a cikin kasafin kudin duk shekara,da kuma irin ci gaban da ake samu a aikace-aikacen da aka bayyana za a yi.
Gidajen yada labarai kuma su bayar da labarun irin nasarorin da aka samu a bangaren, su kuma fallasa munanan ayyukan da ake yi duk a bangaren.
Tabbas Shugaba Tinubu ya bude kofar farfado da bangaren kiwon lafiya a Nijeriya wanda aka yi watsi da shi na tsawon shekaru masu yawa. Amma kuma nasarar wannan aikin ta ta’allaka ce a hannun dukkan masu ruwa da tsaki a bangaren, samar da issassun kudade da kuma sa ido a kan yadda ake kashe kudaden da aka ware.