Rundunar ‘yansanda a jihar Kaduna, ta ce jami’anta sun kama wasu mutane biyu dauke da buhunan taki 600 da ake zargin na sata ne.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Kaduna.
- Mutane 6,000 Sun Amfana Da Zakka Ta Miliyan N132 A Masarautar Hadejia – Kakakin Masarautar
- Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa Ya Shaki Iskar ‘Yanci Bayan Biyan Kudin Fansa Miliyan N10
Hassan ya ce, rundunar ta samu bayanan sirri ne a ranar 8 ga watan Disamba, 2023, cewa an ga wata babbar mota dauke da kayan da ake zargin an sato ne ta kama hanyar Zaria zuwa Kaduna.
“Bayan samun labarin, kwamishinan ‘yansanda (CP), Ali Dabigi, ya umurci tawagar jami’an da ke karkashinsa (CP Monitoring Unit), da su gaggauta amsa kiran gaggawar.
Hassan ya kara da cewa, da isar jami’an wurin suka cafke wanda ake zargin, kuma binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa, wani ne Rigasa da ke karamar hukumar Igabi ya sato kayan, wanda shi ma jami’an ‘yansandan sun kama shi kuma yana taimaka wa ‘yansanda da sauran bayanan sirri.
Ya ce, CP ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da baiwa ‘yansanda goyon baya da bayanai masu amfani akan lokaci da za su ba su damar samun nasarar yaki da duk wani nau’i na miyagun laifuka a jihar.