A wannan sabuwar shekarar za a buga babbar gasar cin kofin kasashen Afirika a kasar Cote’d’Ibore.
Tun da farko dai an shirya gudanar da gasar a kasar Guinea kafin a canza zuwa kasar Cote’d’Ibore. Bayan da kasar ta Guinea ta kasa gudanar da shirye shiryen da ake bukata.
Manyan kamfanonin da za su dauki nauyin wannan gasar ta bana sun hada da Ecobank, Razzi, Apsonic da kuma TECNO, wanda za su hada kai tare da kamfanonin Totalenergies da Orange domin daukar nauyin gasar.
- Babban Jami’in Diplomasiyyar Sin Ya Takaita Abubuwan Da Hadin Gwiwar Sin Da Amurka Ya Kawo
- AFCON 2023: Kasar Da Ta Lashe Gasar Kofin Afirka Za Ta Samu Kyautar Naira Biliyan 6.53
Mawakiyar Nijeriya Yemi Alade da wani mawaki daga Kasar Masar ne za su gabatar da wakokin da za su kayatar da masu kallo a ranakun farawa da rufe gasar ta AFCON.
Kasashe 24 ne suka samu damar buga wannan gasar ta bana da suka hada da: Ibory Coast, Algeria, Morocco, South Africa, Senegal, Burkina Faso, Tunisia, Egypt, Zambia, Ekuatorial Guinea, Nigeria, Guinea Bissau.
Sauran su ne; Cape Berde, Mali, Guinea, Ghana, Angola, Tanzania, Mozambikue, Congo, Mauritania, Gambia, Cameroon da Namibia.
Za a buga wasannin a manyan filayen kasar Cote’d’Ibore har guda 6, sannan kuma an tanadi alkalan wasa har 32 da za su jagoranci gasar.
Za a fara gasar a ranar 13 ga watan Janairu 2024 a babban filin wasa na Alasanne Outarra inda kuma nan za a buga wasan karshe a ranar 11 ga watan Fabrair.
A halin da ake ciki kuma, an tabbatar da dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Royal Antwerp ta kasar Belgium Alhassan Yusuf a matsayin wanda zai maye gurbin Wilfred Ndidi a cikin tawagar Nijeriya a gasar cin kofin Afrika na 2024.
Yusuf wanda tun farko yana cikin yan wasan da aka fitar na wucin gadi ta Super Eagles mai mutum 41.
Wannan dai shi ne karon farko da dan wasan ya samu kira domin wakiltar Nijeriya.
Ndidi ya samu rauni kafin wasan da Leicester City ta doke Huddersfield Town da ci 4-1 a ranar Litinin.