Shahararren dan wasan kwallon kafa na Ghana, Andre Ayew, ka iya kafa wani babban tarihi a gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON) na shekarar 2024 mai zuwa a kasar Ivory Coast.
Dan wasan mai shekaru 34, wanda ya koma kulob din Le Havre na kasar Faransa a kwanan baya, yana da burin zama dan wasa na farko da ya zura kwallo a raga a mabanbantan gasar cin kofin Afrika har sau bakwai.
- Zamu Dogara Da Osimhen Don Lashe Gasar AFCON – Peseiro
- AFCON 2023: Kasar Da Ta Lashe Gasar Kofin Afirka Za Ta Samu Kyautar Naira Biliyan 6.53
A halin yanzu Ayew yana da tarihin zura kwallaye a gasar AFCON shida tare da takwaransa na kasar Ghana Asamoah Gyan,Kalusha Bwalya na kasar Zambia da kuma tsohon kyaftin din tawagar kasar Kamaru Samuel Eto’o.
Bugu da kari, Ayew yana fatan samun damar zama dan wasa na uku kacal da ya halarci gasar har sau takwas,idan hakan ta faru zai zama dan wasa na uku da yayi wannan bajintar bayan Rigobert Song da Ahmed Hassan.