Gwamnatin Tarayya ta hannun Ma’aikatar Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, ta hada hannu da manyan kamfanoni a karkashin shirin farko na tsarin sarrafa sukari na kasa don dakile hauhawar farashin sukari da kuma inganta kamfanonin da ke samar da sukari da ke cikin gida Njeriya.
Ministan Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Dr. Doris Uzoka Anite ce ta bayyana hakan bayan wata ziyarar aiki da ta kai zuwa kamfanonin samar da sukari.
- Kotu Ta Raba Auren Shekaru 7 Saboda Rashin Soyayya
- Wata Mata Ta Sace Jariri Sabuwar Haihuwa A Asibiti A Nasarawa
Ministan a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba ta ce, an dauki matakin ne don samar da daidaiton farashin kayan masarufi, musamman a lokacin azumin Ramadan mai zuwa.
Watan Ramadan mai alfarma, wata ne da musulmin duniya ke ware wa domin azumi da addu’o’i, ana sa ran za a fara azumin ne daga ranar 10 ga Maris zuwa 9 ga Afrilu, 2024.
A mafi yawan lokuta, farashin sukari da na kayan masarufi yana ƙaruwa sosai saboda karuwar bukatar kayayyakin.
A cewar sanarwar, ministan ta ziyarci kamfanonin Dangote Sugar Refinery Plc, BUA Sugar Refinery Ltd, Flour Mills Limited, Bestaf Ltd, da kuma kamfanin Golden Sugar.