Manoman gyada za su iya sa wa a tatse musu man jikinta tas, su sayar tare da samun gwaggwabar riba, duk da dai ya danganta da yawan gyadar da aka tatse man nata.
Ko shakka babu, ana matukar samun riba a noman gyada, dalili kuwa duk manomin da zai iya noma kadada daya, to kuwa zai iya samun akalla tan biyar.
Kalubalen Da Manoman Gyada Ke Fuskanta:
Akwai rashin kayan noman gyada na zamani da kuma rashin sanin kasuwar da ta dace manoma su kai domin sayarwa tare da rashin samar da hukumar da take tantance farashin amfanin gonar.
Har ila yau, akwai kuma kalubalen samun kyakkyawan yanayi maras dadi, wanda hakan ke shafar noman nata tare da rashin wadatattun kudade a hannun manoman, kana kuma da rashin kayan noma na zamani, musamman ganin cewa; akasarin manoman gyadar masu karamin karfi ne.
Wadannan kalubale da sauransu, ya sa suke ci gaba da yin noman gyadar ta hanyar yin amfani da kayan noma na gargajiya.
Wace Jiha Ce A Nijeriya Ke Kan Gaba Wajen Noman Gyada?
Bincike ya tabbatar da cewa, Jihar Biniwe ce a fadin wannan kasa ke kan gaba wajen noman gyada, domin kuwa a shekarar 2005, manoma a jihar sun noma kimanin tan dubu 358,6 1000.
Har ila yau, wannan adadi ya bayyana jihar a matsayin wadda ta noma kimanin kashi 13.68 a cikin 100 a duk fadin Nijeriya.
Matakan Da Manoman Gyada Za Su Dauka Yayin Noma Ta:
Zabar Gonar Da Za Su Shuka Ta:
Wannnan shi ne mataki na farko da ake bukatar manomi ya fara da shi kafin fara yin noman gadan-gadan, musamman domin tabbatar da kasar noman ita ce wacce ta fi dacewa ya yi noman gyadar da ita.
Lokacin Shukata:
A nan manomi zai fara yin shuka ne, a lokacin da kasar noman ke da danshi, musamman a kakar noman damina, inda a lokacin yin shukar ake bukatar ya zuba mata takin gargajiya, don amfanin ya kara habaka.
Lokacin Yi Mata Girbi:
Yi wa gyada girbi na da matukar wahala, sannan ana kashe kudade da dama, haka kazalika ta na kai wa daga wata hudu zuwa Biyar kafin ta nuna baki-daya, inda kuma ake girbin ta yayin da ganyenta ya fara sauyawa zuwa kalar ruwan kasa.
Har ila yau, bayan an girbe ta, ana bayar da shawarar adana ta a inda ba za ta lalace ba, sannan kuma bayan yin girbin za a iya sake yin wata sabuwar shukar; duk a cikin kakar wannan shekarar da aka yi noman gyadar aka yi girbi.
Ban Ruwa:
Ana iya amfani da fanfon ban ruwa wajen yi wa gyada ban ruwa, inda wannan hanya ce tafi saukin yin ban ruwan ga manoman gyadar.
Buhun Gyada Nawa Ake Samu A Duk Kadada Guda?
A duk kadadar noma daya, ana samun buhun gyada daga uku zuwa takwas, inda kuma take kai wa watanni uku kafin a girbe ta, haka nan an fi son a shuka gyadar da ake kira a turance ‘Manipinta’, musamman ganin cewa, ita ce nau’in babba; sakamakon yawan amfanin da ake samu daga gare ta, sannan a duk kadada daya ana samun buhu goma sha biyu.
Mafi yawan lokuta, idan aka yi girbin gyada lokacin rani, sakamakon gwajin da aka samu ya tabbatar da cewa, ana iya samun daga tan .8 zuwa tan 1.8 a duk kadada guda.