Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane 13, ciki harda shugaban masu unguwanni na Karamar Hukumar Yorro, Jauron Wuro Musa a Jihar Taraba.
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Taraba, SP Usman Abdullahi Jada, ne ya tabbatar da faruwan lamarin ga manema labarai a ranar Litinin.
- Ministan Wajen Kasar Sin Ya Yi Tsokaci Kan Yanayin Da Ake Ciki A Shiyyoyi Daban Daban
- Kasashe Da Dama Na Adawa Da Yunkurin Ware Taiwan Daga Babban Yankin Kasar Sin
Mutane sama da 1000 ne suka yi gudun hijira sakamakon hare-hare akauyukansu akalla 35 da ‘yan bindigar suka yi a yankin na Yorro.
Jami’i na musaman mai kula da ‘yan gudun hijira na Karamar Hukumar Yarron, Yarima Usman Abubakar, ya ce a yanzu haka yana da kididdigar ‘yan gudun hijira akalla 1000 wanda suka tantance kuma akwai wasu ma da suke zaune a gidaje a cikin unguwanni a Jalingo.
Mastalar rashin tsaro dai a Nijeriya, sai kara ta’azzara ya ke yi musaman a shiyyar Arewa Maso Tsakiya da kuma Arewa Maso Yamma.