Kwanan baya, jaridar SCMP ta yankin Hongkong na kasar Sin ta wallafa wani sharhi dake cewa, Amurka ta kasance kasa mafi yawan zuba kudade a fannin tsaro, tun kafuwarta zuwa yanzu, ta kwashe kashi 93% na lokutanta tana shiga yake-yake, sabanin yadda take ikirarin zama mai son zaman lafiya da tsaro a duniya.
Amma me ya sa ‘yan siyasar Amurka suke son tada rikici da shiga yake-yake a duniya?
Dalilin shi ne, kudade. Rukunin masana’antun samar da makamai na Amurka da aka san shi da sunan AMIC yana cin mummunar riba sakamakon yadda kasar take tada yake-yake da rura wutar rikici a sassan duniya. Hakan ya sa, wannan sana’a ke da babban muhimmanci ga tattalin arzikin kasar Amurka, duk da cewa hakan na haifar da barazana ga tsaron duniya. (Mai zane da rubutu: MINA)