Satar mutane ana garkuwa da su da nufin karbar kudin fansa ta ta’azzara a ‘yan kwanakin nan bisa yadda masu aikatawa ke cin karensu babu babbaka tun daga arewaci har kudancin kasar nan.
Aika-aikar da suka yi da ta kara tayar da hankulan jama’a ita ce sace wasu iyalai shida tare da mahaifinsu, Alhaji Mansoor Al-Kadriyar, a ranar 9 ga Janairu, a gidansu da ke Zuma 1, a wajen Garin Bwari da ke Abuja. Bayan an sako mahaifinsu domin ya biya fansar Naira miliyan 60, kwatsam a ranar Jumma’a aka wayi gari sun kashe daya daga cikin iyalan, Nabeeha Al-Kadriyar, dalibar Jami’ar ABU tare kara yawan kudin fansar zuwa Naira miliyan 100, saboda sun ji al’umma sun yi karo-karo za a biya Naira miliyan 60 da suka nema da farko.
- ‘Yansanda Sun Cafke Wasu Mutane Biyu Da Ake Zargi Da Satar Keke-napep A Kano
- Ba Wanda Zai Iya Kawo Tsaiko Ga Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
Bugu da kari, ana fargabar wadanda suka yi garkuwa da mutum 10 daga rukunin gidaje na Sagwari Layout, da ke Dutse a Abuja, ranar 7 ga watan Janairu, 2024, sun kashe uku daga ciki kana suka kara kudin fansar daga Naira miliyan 60 kowane mutum daya ya koma miliyan 100.
A yanzu dai kusan kowace karamar hukuma a yankin Abuja tana fuskantar ta’addancin masu garkuwar in ban da kwaryar birnin na Abuja.
Haka nan a makwabciyar Abuja, Jihar Neja, an sace mutum 17 a kauyen Garam da ke Karamar Hukumar Tafa, ranar Larabar makon nan. Bugu da kari, a ranar Alhamis ta makon jiya, da rana tsaka (misalin karfe 3:30 na rana), wasu mutane dauke da makamai suka yi awon gaba da fasinjoji kusan 45 a cikin manyan motocin haya guda uku a Orokam, kan hanyar Otukpo zuwa Enugu dake Karamar Hukumar Ogbadigbo ta Jihar Binuwe.
A Jihar Zamfara ma a ranar Lahadin da ta gabata masu garkuwar sun je garin Magizawa cikin Karamar Hukumar Kauran Namoda inda suka yi awon gaba da mata 36, gami da kashe mutum uku.
Jihar Kaduna ma ba a kyale ta ba, domin kwana nan ‘yansanda sun yi gumurzu da ‘yan ta’addan da suka rufe babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja na tsawon miniti 45, koda yake ‘yandandan sun musunta cewa an sace mutane a wurin.
Haka nan a Jihar Katsina ma ‘yan ta’addar sun kai hari a Garin Nahuce, cikin Karamar Hukumar Batsari, inda suka kona motocin da ke ajiye a wani sansaninsu. Daga can kuma sai suka yada zango a shagunan mutane da gidaje inda suka sace kaya da dabbobi da suka kai na milyoyin Naira.
Wakazalika, a ranar Talata, an bayar da rahoton sace wasu ‘yan mata biyu da ke kan hanyarsu ta komawa makaranta a Jami’ar Alkalam da ke Katsina.
Garkuwa da mutane a shekarun baya-bayan nan
An kiyasata cewa, tsakanin Yulin 2022 zuwa Yuni, 2023, an sace mutum 3,620 cikin farmaki 582 da masu garkuwa suka kai tare da neman kudin fansa akalla Naira biliyan 5 da kuma biyan kudin fansa sama da Naira miliyan 302, adadin da zai iya karuwa, bisa rahoton mizanin SB Morgan.
Ko da yake rahoton ya nuna cewa yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya sun fi shiga matsala, amma yanzu yanayin garkuwa da mutane ya fantsama zuwa wasu jihohin Kudu-maso-Yamma, inda jihohin Legas da Ogun suka fi fuskantar lamarin.
A farkon Disambar 2023, dangin wata ‘yar makaranta ‘yar shekara 13 mai suna Miracle Adereti, sun yi kira ga ‘yansanda da su gano inda ‘yarsu take, wadda wasu ’yan daba suka yi garkuwa da ita a yankin Ikotun na Jihar Legas.
An ce an yi garkuwa da Miracle ne a lokacin da take dawowa daga makaranta, kuma an gano cewa masu garkuwar sun bi ta zuwa makaranta tun da safe suka jira har zuwa lokacin tashi.
Wani lamari kuma da ya faru a Legas shi ne na sace wani dillalin mota da aka fi sani da Ejike Conbersion a Kasuwar kayayyakin gyara ta Ladipo, a tsakiyar watan Disamba. An dai ce Ejike yana daukar lissafin sabbin kayan da ya shigo da su a kofar filinsa da misalin karfe 12 na dare, sai wasu ‘yan bindiga suka kai masa farmaki tare da ma’aikatansa.
Yayin da ma’aikatansa suka gudu domin tsira da rayukansu sakamakon karar harbe-harbe, Ejike bai samu nasarar guduwa ba, ‘yan bindigar suka far masa, suka ja shi cikin motarsu, suka tafi da shi.
A wani lamari makamancin haka, an yi zargin cewa an yi garkuwa da wani dan kasuwa da har yanzu ba a bayyana sunansa ba a farkon watan Janairu a yankin fadar Ago da ke jihar yayin da masu garkuwa da mutane suka bukaci a biya su Naira miliyan 500.
A halin da ake ciki kuma, a yankin Ijebu da ke Jihar Ogun, an samu rahoton an yi garkuwa da wani manomi mai shekaru 70 kuma dattijo a cocin Redeemed Christian Church of God, mai suna Pa Adeife Ifelaja.
An yi garkuwa da wannan tsoho ne a gidansa a ranar 31 ga watan Disamba yayin da yake shirin gudanar da addu’o’in shiga sabuwar shekara.
An yi garkuwa da shi na tsawon kwanaki tara inda suka bukaci a biya su Naira miliyan 50.
Haka kuma, an yi garkuwa da fasinjoji akalla 10 da ke tafiya kan hanyar Ette – Umuopu Enugu-Ezike a Karamar Hukumar Igbo Eze ta Arewa a Jihar Enugu, Kudu maso Gabas, a ranar 15 ga Disamba, 2023.
A ranar 2 ga Disamba, 2023, wasu ‘yan bindiga sun sace wani limamin cocin Katolika, Kingsley Eze, tare da direbansa a Jihar Imo.
A ranar 8 ga Janairu, 2023, wasu mutane dauke da bindiga kirar AK-47 sun yi garkuwa da mutum sama da 30 daga tashar jirgin kasa a Jihar Edo.
Haka nan, wasu ‘yan bindiga sun kuma kashe mutum takwas tare da yin garkuwa da akalla mutum 60 a wasu kauyuka biyu na Jihar Zamfara a ranar 24 ga Satumba, 2023, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
A ranar 23 ga Agusta, 2023, wasu gungun mata manoma 42 ne ‘yan ta’addar Boko Haram suka yi garkuwa da su a Jihar Borno.
Mazauna Abuja Sun Dora Alhakin Lamarin Kan Jami’an Tsaro
Mazauna Babban Birnin Tarayya Abuja sun nuna rashin gamsuwarsu da yadda hukumomin tsaro ke ikirarin magance yawaitar garkuwa da mutane a Babban Birnin Kasar.
Sun ce hukumomin Babban Birnin Tarayya Abuja da na ‘yansanda ba sa yin abin da ya dace wajen kare su da kuma tabbatar da ba wa babban birnin kariya.
Daya daga cikin mazauna Wilfred Akikayo, wanda ya bayyana yadda garkuwa da mutane ta yi kamari a Dutse, ya ce lokacin da aka sace mutane a rukunin gidajen Sagwari da misalin karfe 7:30-8 na dare, sai da aka kwashe kusan mintuna 20 kafin wasu ‘yansanda kwantar da tarzoma (MOPOL) uku dauke da makamai suka fito.
“Idan masu garkuwar suka zo, abu na faro da za su fara yi shi ne buga kofa, kuma duk wanda ya bude to babu makawa sai an yi garkuwa da shi. Wata mata ta gudu daga daya daga cikin gidajen da suka shiga zuwa cikin wani otal da ke cikin estate, inda hakan ne kuma ya kai ga yin garkuwa da biyu daga cikin ma’aikatan otal din.
“Daga baya an sanar da hukumar DSS, da kuma wasu jami’an kuma sun zo bayan minti 30, suka yi harbin bindiga a cikin tsaunuka wai ko a samu martani daga masu garkuwa da mutanen inda ta haka ne za a iya sanin inda suke amma ina.
“A da FCT ne wuri mafi aminci a Nijeriya, amma yanzu, wuri ne mai ban tsoro duba da yadda ‘yan ta’adda suke kara kara karfi, babban abin takaicin shi ne, yadda da suke kara kusantar birnin. Muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kara zage damtse wajen samar da dawwamammen zaman lafiya da kuma mafita dangane da batun garkuwa da mutane da kuma fashi da makami,” in ji shi.
Mazauna yankin na Sagwari da aka kai su bango sun kammala shirin gudanar da gagarumar zanga-zangar tir da yadda gwamnati da jami’an tsaro ke rikon sakainar kashi da matakin ceto al’ummarsu.
Sai dai an dage zanga-zangar da aka shirya yi a ranar Litinin sakamakon bikin tunawa da ranar sojoji ‘yan mazan jiya.
Har zuwa lokacin rubuta wannan labari, masu garkuwa da ‘ya’yan Alhaj8i Mansoor Al-Kadriya ba su sako su ba duk da cewa Tsohon Ministan Sadarwa Da Tattalin Arziki Na Intanet, Isa Ali Pantami da wani abokinsa sun yi alkawarin bayar da Naira miliyan 50.
An ruwaito daya daga cikin kawun wadanda aka sacen, Sherifdeen Al-Kadriyar, ya yi ikirarin cewa masu garkuwar sun yi barazanar kashe sauran ‘yan matan da ke hannunsu idan har ba a biya su kudin fansa Naira miliyan 100 ba.
Sai dai wani babban jami’in ‘yansanda, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce, shigar Pantami da kuma sanarwar da ya yi ya kara dagula matsalar wadanda abin ya shafa domin masu garkuwa da mutane za su kara tsauwala bukatunsu.
Majiyar ta ce abin da ministan ya yi shi ne taimaka wa wadanda abin ya shafa. Amma kuma sanar da taimakon da za su yi a bainar jama’a, ya kara ba masu garkuwar damar kara yawan abin da suke nema.
Sai dai sanar da jama’a na nufin bai wa masu garkuwa da mutane damar yin ciniki don samun kari.
Martanin Wani Babban Soja Mai Ritaya
Wani babban jami’in soja mai ritaya ya ce Abuja ba ta da ‘yansanda na kashin kanta amma duk da haka manyan mutane na yin tafiya bisa rakiyar cincirindon ‘yansanda, lamarin da ke barin sauran ‘yan kasa cikin halin rashin tabbas a kan tsaro.
“Akwai gyara sosai game da tsarin a kewayen Abuja. Na farko, Abuja ba ta da isassun ‘yansanda! amma duk da haka har yanzu suna yi wa daidaikun jama’a ne hidima a maimakon aiwatar da cikakken tsarin da ya kamata.
“Misali, dubi yadda ake shiga cikin Abuja ta manyan hanyoyin Zuba; Mararaba, da Gwagwalada; wane ne yake sa ido a kan tsaron shiga da fita? Za ku lura cewa kasancewar ‘yansanda a wuraren ba shi da wani mahimmanci, saboda ana ganin turawa ne kawai tare da Hanyar Filin Jirgin sama lokacin da Shugaban Kasa ko manyan mutane ke tafiya suke da muhimmanci “.
Ya ce duk da cewa aikin tsaron cikin gida na ‘yansanda ne, amma ya kasa gane hakan, bisa yadda ake amfani da sojoji. Ya tambaya ko manyan mutane ne kawai ke da hakkin samun kariya daga ‘yansanda?
“Sannan shugabanninmu sukan ba sa ganin wadannan barnace-barnace da ake yi saboda suna da masu yi musu rakiya. To yaya kuma lamarin yake game da al’umma? Shi ya sa na ce babu bukatar bata lokaci wajen magana. Ba da gaske muke ba game da kula da harkar tsaronmu”.
Ya kara da cewa sojoji za su taimaka ne kawai bisa tsarin mulki cikin kankanin lokaci, yayn da ‘yansanda suka gamu da cikas suna neman dauki amma ba dindindin ba.
Abin Ya Zama Annabo A Nijeriya – Kungiyar Kare Hakkin Dan’Adam
Kungiyar Kare Hakkin bil-Adama ta Kasa da Kasa ‘Amnesty International’, a ranar Litinin da ta gabata ta bayyana cewa a halin yanzu sace-sacen mutane ana garkuwa da su ta zama annoba a Nijeriya.
Ofishinta na Nijeriya ya bukaci Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ta dauki wannan annoba a matsayin abin da ya shafi kasa yake bukatar dauki cikin gaggawa.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce, “Dole ne Shugaba Bola Tinubu ya dauki yawaitar garkuwa da mutane da ya zama wani bangare na rayuwar yau da kullum a Nijeriya a matsayin abin da yake bukatar daukar matakin gaggawa da suka dace don kawo karshen tashe-tashen hankula da fargabar jama’a a Nijeriya.”
“A makon da ya gabata an yi garkuwa da mutum sama da 45 da ke tafiya tsakanin Otukpo da ke Jihar Binuwe da Enugu, kuma har yanzu ba a ji labarinsu ba.
“Haka nan a makon da ya gabata, masu garkuwa sun kashe daliba Nabeelah saboda danginta ba za su iya gaggauta biyan bukatar masu garkuwa da mutane na neman kudin fansar Naira miliyan 60 ba. ‘Yan uwanta har yanzu suna hannun masu garkuwa da mutane.
“Haka nan an kashe daya daga cikin mutum 10 da aka yi garkuwa da su a wani katafaren gida da ke Dutse kusa da Abuja saboda gaza biyan kudin fansa.”
Isa Sanusi, Daraktan Kungiyar Amnesty International a Nijeriya, ya zargi gwamnatin kasar da rashin yin abin da ya dace wajen dakile wannan alkaba’i.
“Yanzu muna fuskantar annobar garkuwa da mutane. Jama’a a Nijeriya suna rayuwa a cikin fargaba. Rashin tsaro da rikice-rikicen sun kara ta’azzara ta hanyar sace-sacen jama’a a yau da kullum, yayin da kungiyoyi masu dauke da makamai suka tsaurara kai hare-hare a kasar.
“Dole ne hukumomin Nijeriya su gaggauta dakile matsalar garkuwa da mutane a yanzu.
“Iyalai da yawa sun yanke shawarar kin bayar da rahoton satar mutane bayan sun biya kudin fansa saboda tsoron ramuwar gayya kuma a sakamakon haka abubuwa da yawa ba sa tafiya daidai. Annobar garkuwa da mutane a halin yanzu ta nuna gazawar mahukuntan Nijeriya wajen kare rayuka yadda ya kamata.
“Ba a san adadin mutanen da ke hannun kungiyoyi masu dauke da makamai da masu garkuwa da mutane ba. Amma wadanda abin ya shafa sukan fuskanci cin zarafi mai ban tsoro. Mata da ‘yan mata da dama, ciki har da yara ‘yan makaranta, an yi musu fyade yayin da ake tsare da su. “Ana azabtar da wadanda aka sace a kai-a kai. Ana yi wa da yawa duka, da barin su da yunwa, barazanar kisa, fyade, rufe idanuwa na kwanaki da dama, da sauransu.
“Hukumomin Nijeriya har yanzu ba su nuna wani kudiri na gaske ba don magance tabarbarewar tsaro a fadin kasar. Duk matakan tsaro da ake aiwatarwa a halin yanzu a fili ba sa aiki. Tsaron mutane ya kamata ya zama fifiko a wurin gwamnati. Rashin magance matsalolin tsaro cikin gaggawa zai ba da damar cin zarafin bil’adama sosai,” in ji sanarwar.
Tinubu Ya Gana Da Shugabannin Tsaro, Ya Ce Ilmantar Da Matasa Zai Rage Matsalar
Shugaban kasa Bola Tinubu, a ranar Talata ya gana da hafsoshin tsaro da sauran shugabannin hukumomin tsaro a fadar gwamnati da ke Abuja, kan karuwar rashin tsaro.
Taron ya samu halartar babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Christopher Musa; Babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja; Babban hafsan sojin ruwa, Bice Admiral Emmanuel Ogala; Hafsan Hafsoshin Sojan Sama, Air Marshal Hassan Abubakar; Babban sufeto na ‘yansanda, Kayode Egbetokun, da sauran shugabannin hukumomin tsaro.
Duk da cewa ba a fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan taron, amma ana kyautata zaton cewa, shugaba Tinubu da hafsoshin tsaronsa sun yi nazari kan al’amuran tsaro a sassan kasar nan, inda za su sake shiri kan fatattakar ‘yan ta’adda.
A halin da ake ciki kuma, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta fara shirin ilimantar da matasa a matsayin daya daga cikin hanyoyin magance matsalar tsaro da ta addabi wasu yankunan kasar nan.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a wajen taron kaddamar da littafin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Sai dai har yanzu ana ci gaba da kai munanan hare-hare musamman a Arewacin Nijeriya duk da alkawarin da shugaban ya yi a lokacin yakin neman zabensa.
Yanzu haka babban birnin tarayya, Abuja na fuskantar karuwar sace-sacen mutane a manyan tituna da kuma gidaje a baya-bayan nan.
Tinubu ya yi Allah-wadai da sace-sacen da aka yi na baya-bayan nan sannan ya kudiri aniyar kawo karshen lamarin.
“Babu wani makami da zai yaki talauci da ya kai karfin ilimi,” in ji shi.
“Hukumomin tsaro suna aiki tare da tura dakaru don magance kalubalen da ake fuskanta nan da nan, yayin da kuma za a samar da dukkan abubuwan da ake bukata, da manufofi da tsare-tsare nan ba da jimawa ba don ilimantar da matasan Nijeriya.”
Yanzu haka dai, mazauna wajen Abuja, sun fara yin hijira a daidai lokacin da ake samun yawaitar sace-sacen mutane don neman kudin fansa.