Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce kasarsa ta shirya kara kulla dangantaka da kasashe kamar na Australia da New Zealand game da batun kasashen tsibirin Fasifik
Wang Yi ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da firaministan Samoa kuma ministar harkokin wajen kasar, Fiame Naomi Mata’afa, a birnin Apia, fadar mulkin kasar.
A cewarsa, dangantaka tsakanin Sin da kasashe masu tasowa ko kasashen tsibirin Fasifik ba ta nufin musgunawa wani bangare, kuma Sin ba ta neman wasu hakkoki na musammam. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa)