Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken ya bayyana shirin kasarsa na taimaka wa Yammacin Africa da dala miliyan 45 don yaki da ta’addanci da kuma tabbatar da tsaro.
Blinken na wadannan kalamai ne lokacin da y gana da shugabannin kasashen Nijeriya, Cape Verde da Angola , a ziyarar kasashen Nahiyar Afirika da ya fara.
- Gwamnatin Tarayya Ta Kafa Kwamitin Sa ido Kan Tsaro A Hanyar Abuja Zuwa Kaduna
- Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Tsarin Ddoka Da Matakan Yaki Da Taaddanci
Manufar ziyarar dai ita ce tattauna alaka musamman ta kasuwanci tsakanin Amurka da kasashen Yammacin yammacin Afrika, sauyin yanayi, lafiya, tsaro da sauran matsaloli.
Ziyarar Blinken na biyo bayan taron shugabannin kasashen Afrika da ya gudana a birnin Washington a watan Disamban 2022.
Yayin da yake jawabi a kasar Cape Verde, Blinken ya ce yanzu lokaci ne da duniya ke sha’awar mu’amala da Afrika don haka ba za a bar Amurka a baya ba, la’akari da muhimmancin da Afrika ke da shi da kuma tarin arziki.
Kusan dukannin kasashen Yammacin Africa na fama da matsalolin tsaro da suke da alaka ta kai-tsaye da kungiyoyin masu ikirarin jihadi.