Malaman makarantun Firamare a Abuja, sun gudanar da zanga-zanga a dandalin “Unity Fountain” da ke kan rashin biyan su albashi.
A yayin zanga-zangar, malaman sun zargi Kananan Hukumomin Abuja kan rashin kula da jin dadi da walwalarsu.
- Gwamnatin Tarayya Ta Kafa Kwamitin Sa ido Kan Tsaro A Hanyar Abuja Zuwa Kaduna
- INEC Za Ta Gudanar Da Zaben Cike Gurbi A Rumfunan Zabe 46 Na Jihar Sokoto
Malaman sun gudanar da zanga-zangar ne kan rashin biyan su bashin da suke bi na kudaden da na karin girma da kuma na mafi karancin albashi tun daga shekarar 2019.
Malaman sun bukaci Ministan Abuja, Nyesom Wike da Shugaban Kasa Bola Tinubu su sa baki a kan lamarin.
Haka kuma sun yi kira da a sake duba tsarin ilmin Firamare a kasar nan, inda suka bukaci gwamnatin tarayya ta kwace ragamar gudanar da makarantun daga hannun kananan hukumomi.
Malaman sun shafe fiye da mako guda suna yajin aiki amma har yanzu sun ce babu wani takamaiman martani daga hukumomin da al’amarin ya shafa.