Rundunar mafarauta a jihar Kano da ke kula da tsaron dazuka (NHFSS) ta ce, ta samu korafe-korafe 19 a watan Janairu.
Kwamandan NHFSS na jihar, Malam Abdullahi Al-Ameen, ne ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) a ranar Alhamis a Kano.
Ya ce, hukumar na kokarin ganin ta bar aikin ta na hana miyagun laifuka a dazuzzukan jihar.
“Daga cikin masu korafin 19, 15 an yi shawo kannau yayin da ragowar hudun ake kan shawo kansu.
“Yawancin matsalolin suna da alaka da satar dabbobi da sace-sacen waya da sauransu.
“Muna yi ƙoƙari don ganin mun kawar da laifuka daban-daban d ake aikatawa a cikin daji a cikin,” Cewarsa.
Al-Ameen ya roki hadin kan al’umma wajen ganin jihar ta zama samu kubuta daga masu aikata laifuka.