Halin da Nijeriya ta samu kanta a bangaren matsatsin rayuwa da tsadar kayan masarufi a wannan lokacin musamman tun wajajen karshen shekararar 2023 da zuwa 2024 na kara jefa ‘yan kasan da ita kanta kasar cikin ukuba. Baya ga hakan, zamantakewar aure ma na fuskantar babban barazana sakamakon yadda yanayin rayuwa ya yi tsada sosai.
Wani bincike da LEADERSHIP Hausa ta gudanar, ya nuna cewa kusan komai na kayan bukatar rayuwa sun yi tashin gwauron zabi, lamarin da ke tilasta wa mutane rage burace-burace, yana hanasu jin dadin rayuwa. A bisa haka ne, lamarin zamantakewar aure ke kara shiga garari. Yayin da wasu dubban matasa ke zaman jiran samun yanayin da ya dace su yi aure, amma sakamakon halin da ake ciki sun cire rai.
- Kotu Ta Daure Dillalan Miyagun Kwayoyi 15 Shekara 168 A Gidan Yari A 2023 – Marwa
- Rundunar ‘Yansanda Ta Shelanta Neman Dakta Idris Dutsen Tanshi Ruwa A Jallo
Kazalika, a maimakon matasa da ‘yan matasa su samu damar yin aure, sai su tsinci kansu a aikata fasadi domin su matukar son aure babu hali. Yayin da wasu kuma ke tunduma harkokin da ba su kamata ba.
Wannan matsalar dai bai rasa nasaba da tashin dala da kuma tsadar man fetur da ke kara jefa al’ummar Nijeriya cikin damuwa.
A bisa hakan ne LEADERSHIP Hausa ta ji ra’ayin wani masani mai sharhin lamuran yau da kullum, Nazeep Sulayman Ibraheem, inda ya ce, muddin ba a dauki matakan da suka dace ba, nan gaba ma auratayya da daman gaske za su iya rabuwa a kasar nan.
“Hakika hauhawar farashin kayayyakin masarufi na iya haifar da matsaloli da lalata zamantakewar aure wanda ka iya kai wa ga rabuwar autarayya idan ba a tashi tsaye an magance yadda ya kamata ba.
“Matsalolin karancin kudi: Tsadar rayuwa ka iya rage karfin sayen abubuwan bukata da kuma rage wa ma’aurata samun kudaden shiga, lamarin da zai kasance abun wahala a garesu iya mallakar abubuwan bukata na yau da gobe, irin wadannan abubuwan sun hada da kayan abinci, gidaje, da kuma kula da kiwon lafiyarsu. Wannan ka iya janyo takaddama a cikin zamantakaewa, rikici a kan kudi, da kuma jin kawai a rabu domin saukaka wa juna.
A cewarsa, akwai kuma bukatar ma’aurata su kasance masu tsara yadda za su kashe kudadensu da yin tattali hadi da neman shawarorin masana tattalin arziki kan yadda za su cimma burin rayuwarsu na gaba.
Muhammad Sambo Aminu, wani matashi ne dan jihar Kano da ke da shekara 28 a duniya, ya bayyana mana yadda halin kuncin rayuwa ya hana shi yin aure, “A zahiri akwai matsala, ina da budurwa za mu iya kawai shekara kusan uku ko hudu tare, muna son yin aure fiye da yadda kake tunani, amma gaskiya ba zai yiwu na yi aure a halin yanzu ba.
Hajiya Halima M. Ahmed, uwa ce daga Jihar Neja, na cewa, “Matsalar nan fa ta kai lahaula. Yanzu gidaje da dama ba su iya sayen kayan abinci balle a yi maganar aurar da yara. Ina da ‘yan mata “Ya’ya uku” wadanda ko yanzu aka kaisu gidan miji za su zauna, amma babu takamaimai masu nema, kodayake akwai masu neman amma gaskiya ba su da halin aure. In ma masu nemansu sun shirya mu ina muka ga halin aurar da ‘ya’ya uku yanzu? Kayan daki ba su tabuwa, Allah dai ya kawo mana sauki kawai,” ta shaida.
Wani direba da wakilinmu ya zanta da shi a jihar Gombe, Lukman Sambo, ya ce, har Allah-Allah yake yi su samu matsala da matarsa ya korata zuwa gidansu, “Kwana biyu kafin yau mun samu rashin fahimta da matata, har na so na korata gida, sai na ce bari na jira ta sake min wani laifi, malam a zahirin gaskiya rashin kudi ne ya janyo fadana da ita. Kodayake yanzu matan ma sun gane, ba su bari a kai gabar hanayi domin wallahi mazaje da dama sun gwammace su raba auren kawai su huta, to nauyi ne a kanka kuma kana shan wahala sai ka sauke a huta kawai,” ya tabbatar.
LEADERSHIP Hausa dai ta labarto cewa hauhawan farashin kayan masarufi ya haura zuwa kashi 28.92 zuwa watan Disamban 2023, wanda hakan na nuni da cewa a sama da shekaru 24 Nijeriya ba ta taba fuskantar irin wannan hauhuwar farashin ba.
A cikin rahoton da hukumar kiddigga ta kasa (NBS) ta fitar a kwanaki, ta ce, zuwa watan Disamban shekarar da muka wuce, hauhawar farashi ya karu zuwa kashi 28.92 daga kashi 28.20 a watan Nuwamba 2023.
Hukumar ta ce, idan aka duba kididdigar hauhawa a Disamban 2022 da ya kai zuwa 21.24 kuma aka kwatanta da na shekarar 2023, za a iya cewa duk shekara Nijeriya na samun karuwar hauhawar farashi.
Hukumar ta cigaba da cewa hauhawar farashin abinci zuwa Disamban 2023 ya kai kaso 33.93 cikin 100 a shekara guda, kaso 10.18 na hauhawa idan aka kwatantanta da na Disamban shekarar 2022 mai kashi 23.75 cikin dari.
Ta ce, hauhawar abincin ya faru ne sakamakon tsadar kayan abinci irin su buredi, mai da man girki, dankali, doya, kayan hatsi, kifi, nama, kayanmarmari, madara, koyi, da dai sauran kayan abincin da ake amfani da su a Nijeriya.
Ita kuma Malama Jummai Ahmad Karofi marubuciyar littafai ce kuma uwa ce daga Jihar Kaduna wacce ta aurar da ‘ya’ya maza da mata sannan ta kasance mai sharhi kan lamuran rayuwa tare da gwanancewa wajen sulhunta ma’auratan, ta bayyana a hirarta da LEADERSHIP HAUSA cewa matsin rayuwa da na tattakin arziki sun kara jefa rayuwa auren mutane da dama ne cikin gariri, tana mai cewa a halin yanzu aure da daman gaske hakuri ne kawai ke rike da su ba wai don ana samun yadda ake so ba.
Ta kuma ce a matsayinsu na iyaye mata sun maida hankali ne kawai wajen rarrashin ‘ya’yansu mata a gidajen mazaje tare da samar musu da tallafin yadda za su rayu domin guje wa yawaitar sake-saken auren da ke faruwa a cikin al’umma.
Ta ce, in ma an samu raguwar mace-macen aure a tsakanin al’ummar Hausawa to tabbas hakuri da kokarin iyaye ne ya jawo hakan domin rayuwa take inganta a kowani lokaci, ta nuna cewa saki na zuwa ne a yanayi na dole ba don ana son hakan ba.
Jummai Karofi na cewa: “Mu yanzu yaranmu da suke kan hanyar a sakesu saboda matsalar rayuwar ba mu san adadinsu ba. Da yaranmu da yaran “yan uwanmu, abu guda kawai da ke zaunar da su a gidajen mazajensu shi ne irin taimakon da mu iyayen muke musu na yadda za su rayuwa. Mazajen wasu guduwa suke yi su bar su.
Hajiya Hauwa Hussaini, shugabar wata kungiyar kare hakkin al’umma ce daga jihar Kano, tana mai bayyana ra’ayinta da cewa matsin rayuwa na tarwatsa wa mata farin cikinsu musamman a gidajen aurensu.
Ta ce, mafi yawan lokuta ana kauce wa hanya ne har a samu saki na shiga don haka ne ta jawo hankalin masu aure da masu son yin aure da suke rungumar dabi’ar hakuri da juna cikin wadata ko rashinsa.
“Idan ka lura an fi samun wannan matsalar a cikinmu Hausawa. Da zarar dan kankanin matsala ta faru kawai za ka ji maganar saki, kuma in an rabu dole wani ko wata za a sake nema. Don haka to meye amfanin hakan? Da zarar aka yi aure kawai abun da ya kamata shine a yi hakuri a zauna da juna lafiya koda wadatar arzikin ko ana cikin matsi. Abu na farko dai kowa ya ji tsoron Allah.
Mu’azu Umar Hardawa wani mazaunin unguwar Fadamar Mada a Bauchi ne kuma dan jarida ne ya bayyana ra’ayinsa da cewa: “Gaskiya ne wahala ta sa mata da dama sun nutsu sun rage haifar da matsala a gidajen aure saboda sanin halin da ake ciki na wahala da tsadar rayuwa sun sa mazan da ke iya rikewa da dawainiyar gida kullum suna kara raguwa. Musamman wanda basu da gidan zama na kansu kullum cikin matsala suke idan samun su ba shi da karfi.
Allah ka yaye mana wahala ka gyara Nijeriya ka dawo mana da walwala da jin dadi, Allah ka bamu shugabanni na gari masu tausayawa talakawa, Amin”.