Wata kungiya mai rajin ci gaban matasan karamar hukumar Rano mai suna “Rano Youth Progressive Association” ta yi kira da majalisar dokokin jihar Kano da ta da yi watsi da batun cire Sarakunan Kano ko sauya wa masarautun fasali.
A cikin wata takardar me dauke da sa hannun shugaban kunggiyar, Ahmed Wada wakili, sun bukaci majalissa da masu fada a ji da su jingine batun ko yunkurin rushe masarautun jihar Kano.
- Makomar Masarautun Kano Ta Fara Tayar Da Kura A Jihar
- Kungiyar ‘Yan Dangwale Ta Nemi Majalisa Ta Tsige Sarakunan Kano 5 Da Dawo Da Sanusi
- Jama’ar Kano Na Ƙaunar Alh. Aminu Ado Bayero Saboda Ƙaunarsa Da Zaman Lafiya
A cikin takardar, kungiyar ta bayyana irin alfanun da wadannan masarautun suke da shi ga al’ummar Kano da kuma irin ci gaba da bunkasar tattalin arzikin yankunan da aka samar da masarauttun suka samar da suka hada da rabon mukamai da wasu albarkatun kasa, kungiyar ta ce yanzu ana kallon masarautu ne ba yankunann santoriya ba.
Idan ba a manta ba, a cikin makon nan an samu wata kungiyar da ta kira kanta da Kungiyar ‘Yan Dangwale, da ta aike da bukatarta na rushe masarautun Kano biyar da gwamnatin da ta shude ta samar, tare da dawo da Sarkin Kano na 14 Muhammadu Sanusi ll kan karagar Sarautar Kano, bisa da’awar kungiyar na cewa ba’a bi doka ba wajen tube rawanin Sarkin.
‘Yan dangwale, sun ce cikin bukatarsu akwai dawo da masarautun Kano biyar kwaya daya rak kamar yadda suke a baya can gabanin rarraba su.