A wata sanarwa da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila ya fitar a baya-bayan nan, ya bayyana cewa shirin bayar da lamuni ga dalibai na gwamnatin tarayya za a kaddamar da shirin nan da makonni biyu zuwa uku masu zuwa.
Wannan tabbacin na zuwa ne a wata ganawa da wakilan kungiyar dalibai ta kasa (NANS) suka yi da shugaban ƙasa a fadarsa da ke Abuja.
- Bashin Ilimi Ga Daliban Nijeriya: Manufar Da Ba Ta Da Kyakkyawar Manufa
- Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Yadda Dalibai Za Su Samu Bashi
Gbajabiamila ya ba da tabbacin cewa, an fara shirye-shiryen wanda ya yi nisa sosai don aiwatar da shirin.
Da yake jawabi game da matsalolin da ke tattare da shirin, Gbajabiamila, ya bukaci dalibai da su bayar da shawarwari wanda za su inganta shirin.
Gbajabiamila ya jaddada muhimmancin shirin a matsayin wani bangare na inganta manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma kudirinsa na bunkasa ilimi.