Shuka Kankana da girbinta, na kai wa kimanin watanni uku; sannan za ka iya shuka ta tare da girbe ta sau akalla hudu a shekara a kuma Fuloti guda, har ila yau za ka iya shuka sama da 1,596.
A yanzu haka, Kasar Chana ce ke kan gaba a fadin duniya wajen noman Kankana, haka nan kuma wani fanni ne da ke samar da kudaden shiga ga wadanda suka rungumi noman a matsayin sana’a, sannan a Nijeriya za ka iya fara wannan noma da Naira 50,000, banda kudin hayar gona.
- Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Kashe Naira Biliyan Ɗaya Don Aikin Kiwon Lafiya Kyauta Ga Marasa Ƙarfi A Jihar
- Da Ɗumi-ɗumi: Bayan CBN, FAAN, Manyan Ma’aikatun Hukumar Man Fetur Na Shirin Komawa Legas
Har ila yau, wanda ya noma fuloti daya; zai iya samun ribar akalla Naira 400,000 a shekara daya kacal, sannan ta na kuma jurewa kowane irin yanayi tare da bijere wa cututtukan da ke harbin amfanin gona.
Tsara Yin Kasuwancinta:
Da farko, idan har ba ka tsara yadda za ka yi kasuwancinta ba, tabbas za ka iya tabka asara mai yawan gaske.
Kazalika, tsarin kasuwancin nata ya hada da aiwatar da kasafin kudin da za ka kashe wajen yin nomanta, inda hakan zai taimaka wa manomin nata wajen samun kudaden shiga masu yawa.
Zabar Ingantaccen Irin Nomanta:
Wannan na daya daga cikin muhimman abubuwan da masu nomanta ya kamata su yi la’akari da shi, musamman a nan Nijeriya, domin kuwa akwai Iri kala-kala; ya danganta da wanda ka ke bukata ka shuka.
Zabo Wajen Shuka Irin:
Shi ma wannan na da matukar muhimmancin gaske duk da cewa, Allah ya albarkaci jihohin kasar nan 36, ciki har da Babban Birnin Tarayyar Abuja da kasar noma.
Sharar Gona:
Mataki na karhe shi ne, sharar gona don shuka Irin Kankana, inda wannnan matakin ya kunshi nome ciyawa, zuba takin gargajiya ko na zamani.
Tsarin Yadda Ake Shuka Irinta:
Wannan ya kunshi yadda ake shuka Iri na Kankana da kuma gyaran gonar da za a shuka Irin, sannan ana so a shuka Irin ta hanyar yin nesa da juna.
Yin Ban Ruwa:
Wajibi ne a tabbatar da an yi ban ruwa yadda ya kamata akalla sau biyu a duk mako, musamman ganin cewa; ta na daya daga cikin amfanin gonar da ke bukatar a yi mata ban ruwa a lokacin da aka shuka ta.
Kare Ta Daga Harbin Kwari Tare Da Nome Ta:
Dole ne a tabbar ana nome mata ciyawa tare da yi mata feshi, domin ba ta kariya daga kamuwa da cututtukan da ke harbin amfanin gona.
Tsarin Yi Mata Girbi:
A nan bayan ‘ya’yan sun girma, sun kai munzalin cirewa; sai a cire su musamman ginin cewa, ta na kai wa daga kimanin kwana 75 zuwa 90 kafin ta nuna.
Adana Ta Bayan Girbi:
Ya na da kyau bayan ka girbe ta, ka tanadi guri mai kyau da za ka adana ta kafin ka kai ta kasuwa, don sayarwa ko kuma samo wanda zai saya, don haka za ka iya adana ta har zuwa tsawon wata daya ba tare da ta yi komai ba, amma kar ka bari ya kasance rana na dukan ta.
Sayarwa:
Za ka iya sayar da Kankanarka baki-daya a lokaci guda, musamman ga manyan shaguna, kasuwanni, kamfanoni ko ga dai-daikun mutane ko kuma ga masu safararta zuwa kasashen waje da sauran makamantansu.