Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Ko Kin San.
A yau shafin namu zai zakolu muku abincin da ya kamata su kiyaye yayin da suke jinin al’ada:
Mata ku kiyaye wadannan abinci guda biyar 5 a lokacin da kuke jinin al’ada, ku kiyaye saboda yana da matukar hadari a lafiyarku.
Wadanne abinci ne?
Ya kamata ku kiyaye shan madara a lokacin al’ada saboda tana da matukar hadari a lafiyar ku.
Ya kama ku kiyaye shan kofi a lokacin al’ada saboda shima yana da hadari ga lafiya.
A duk lokacin da kuke al’ada ya kamata a ce kun kiyaye duk wani abin da yake da zaki saboda zaki yana da matukar illa ga lafiyarku.
Akwai abin da ba kowace mace ce take iya hakura da shi ba, amma kuma yana da matukar hadari ga lafiyarku a lokacin al’ada ya kamata ku nisanci cin Jan nama saboda gujewa faruwar hadari ga lafiyarku.
Sai Barkono shima wannan yana da matukar hadari ga lafiya ku kiyaye cin yaji a lokacin al’ada.