Hon. Abdulkadir Rahis na daya daga cikin ‘yan majalisa mafiya taka rawa wajen wakiltar al’ummarsu.
A baya dai matasa sun taka muhimmiyar rawar gani sosai a sassa daban – daban na ci gaban kasar. Kusan ma za a iya cewa su ne kan gaba wajen tafiyar da al’amuran kasar bayan samun ‘yancinta.
Alal misali, shuwagabanni irin su Janar Murtala Muhammad da Janar Yakubu Gowon, sun shugabanci kasar suna matasa, duk da cewa shugabanci ne na gidan soja, amma kuma sun taka muhimmiyar rawar gani. Haka kuma ko a yau, akwai irin su Abdulkadir Rahis, wanda shi ma matashi ne.
Kimanin shekaru goma sha biyar (15) ke nan, da tsohon dan majalisar birnin Maiduguri mai suna Umara Kumalia, ya wakilci birnin a majalisar tarayya ba a sake samu dan majalisa da ya maimaita wannan kujerar ba, sai Abdulkadir Rahis; wanda yanzu haka yake shirin maimaita kujerar a karo na uku.
Wannan shi ne jadawalin ‘yan majalisun da suka yi wannan kujerar daga 1999 zuwa yau.
Umara Kumalia a karkashin jam’iyyar APP (All People’s Party), daga Mayu 1999 zuwa Mayu, 2003 Miladiyya.
Umara Kumalia karo na biyu a karkashin jam’iyyar ANPP (All Nigeria People Party), daga Mayu, 2003 zuwa Mayu, 2007 Miladiyya. Mustapha Baba Shehuri a karkashin jam’iyyar ANPP (All Nigeria People Party), daga Mayu, 2007 zuwa Mayu, 2011 Miladiyya.
Gujbawu Kyari a karkashin jam’iyyar ANPP (All Nigeria People Party), daga Mayu, 2011 zuwa Mayu, 2015 Miladiyya. Abdulkadir Rahis a karkashin jam’iyyar APC (All Progressibe Congress), daga Mayu, 2015 zuwa Mayu, 2019 Miladiyya. Abdulkadir Rahis karo na biyu a karkashin jam’iyyar APC (All Progressibe Congress), daga Mayu, 2019 zuwa Mayu, 2023.
Abdulkadir Rahis karo na uku a karkashin jam’iyyar APC (All Progressibe Congress), daga Mayu, 2023 zuwa Mayu, 2027 idan Allah ya nufa.
Wane ne Abdukadir Rahis (Kadiri)?
Sunansa Abdulkadir Rahis, ana masa lakabi da Kadiri. An haife shi a shekarar 1968 a cikin birnin Maiduguri. Ya halarci makarantar kimiyya da fasaha ta karamar hukumar Bama wacce ya kammala a shekarar 1989.
Kadiri ya shiga siyasa a shekarar 1990, inda ya zama kansila a unguwar Shehuri South. A shekarar 1997 aka zabe shi a matsayin ciyaman din unguwar Shehuri South a karkashin inuwar jam’iyyar UNDP. A 1999 ya zama ma’aji (Treasurer) na jam’iyyar APP na birnin Maiduguri. Saboda kwarewarsa da iya shugabancinsa, ya sa aka nada shi mai kula da aiyukan kasilolin (Superbisory councilor for work) na birnin Maiduguri daga 2001 zuwa 2003.
A shekarar 2009 aka sake nada shi a matsayin memba a kungiyar kwallon kafa ta Borno, wato El-kalemi Warriors. Bayan ya yi ritaya daga memban, sai ya zama ciyaman din kungiyar. A shekarar 2009 ya sake zama zababben shugaban matasan birnin Maiduguri har zuwa 2011.
A cikin shekarar 2011 gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya nada shi a matsayin mashahurci na musamman ga gwamnan, kafin daga baya ya zama shugaban rikon kwarya a komitini zantarwar na birnin Maiduguri a 2015.
A cikin shekarar 2015 ya zama zababben dan majalisar tarayya mai wakiltar birnin Maiduguri a karkashin jam’iyyar APC, wanda har yanzu yake kan wannan matsayin.
Babban matakin yakar talauci da kuma jahilci shi ne ilimi, wannan ya sa Kadiri ya gina wasu karin ajujuwa a sama da makarantu goma sha hudu da ke birnin Maiduguri.
Bayan haka, yana dauke da nawin karatun matasa da dama a birnin Maiduguri, domin ba su ilimin da za su dogora da shi a nan gaba, saboda kiyaye su daga fada wa kungiyoyin ta’addacin irin su Boko Haram.
Kadiri ya dasa fanfunan ruwa tare da kafa tankunan ruwa na zamani masu aiki da hasken rana (Sola) a unguwannin cikin birnin Maiduguri da suka hada da: Bulabulin da Bolori I da Bolori II da Fezzan da Gwange I da Gwange II da Gwange III da Gamboru Liberary da Hausari/Zango da Limanti da Lamisula/Jabbamari da Maisandari da Mafoni da Shehuri Sourth da kuma Shehuri North.
Sannan kuma yana bawa ‘yan gudun hijiran da Boko Haram suka kora daga karuruwansu tallafi abinci da abin kashewa. Ya kuma samarwa da duban matasan a Maiduguri mashin mai taya uku (Keke napep) domin su tsaya da kafafuwansu ba tare da sun zauna zaman kashe wando ko jiran ganima daga gwamnati ba. Domin hakan ne kadai zai fitar da su daga takaicin rashin aikin yi da zaman kashe wando da ake fama da shi.
Muna fatan alheri tare da addu’ar Allah Ya saka masa da alheri ya kuma ba mu shuwagabani masu kishin mu kamar shi, Amin.