An bayyana cewa Jihar kano ce ke sahun gaba wajen shan Maltina a duk fadin Nijeriya, inda hakan ke da dangantaka da kasancewar Kano a matsayin cibiyar kasuwanci a Arewacin Nijeriya baki daya.
Baya ga wannan kuma jiha ce mai albarka da ta samu kyakkyawan jagoranci, tun shekaru masu yawa da suka wuce. Saboda haka, Kano ta zama gidan Maltina, fiye da kowace jiha a kasar nan.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Manajan kasuwanci mai kula da jihohin Arewa, Alhaji Kabiru Kasim, jim kadan da fitowar ayarin shugabannin Maltina da suka ziyarci fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayeron, domin bunkasa dangantaka da masarautar Kano da gwamnatin jahar da al’umar Kano baki daya, wadanda da su ne kasuwancin Maltina ke tafiya daidai a Kano.
Manajan kasuwanci na Arewa Kabiru Kasim, ya ce saboda haka ne ya sa shi ma kamfanin Maltina ya sa ya kawo ziyara Kano.