Akalla mutum 10 da ake zargin masu safarar mutane ne, da suka hada da mata takwas da maza biyu, rundunar ‘yansandan Jihar Nasarawa ta kama bisa zargin satar yara shida daga sassa daban-daban na kasar nan domin yin kasuwanci.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Umar Nadada, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a garin Lafiya yayin da yake gabatar da wasu mutane 57 da aka kama da aikata laifuka a jihar.
- Babban Jami’in JKS Ya Bukaci A Himmantu Wajen Ciyar Da Kokarin Dunkulewar Kasar Gaba
- Matsayar Sin Game Da Burin Wanzar Da Zaman Lafiya A Duniya
A cewarsa, ‘yan kungiyar 10 sun sace yara 45 tare da sayar da su ga abokan huldarsu kan makudan kudade, gami da shirinsu na sayar musu da kananan yara da suka hada da maza da mata.
Nadada ya ce, “A ‘yan kwanakin nan, jami’an ‘yan sanda da ke aiki da sashen Keffi da ke sintiri na yau da kullum sun ga wani yunkuri na gungun jama’a inda suka shiga domin ceto wanda abin ya shafa.
“Da aka yi bincike, an gano cewa wanda abin ya shafa yaro ne mai suna Ismaila Adamu ya sace wani yaro dan shekara biyar a Tsohuwar Kasuwa, Keffi; Nan take aka garzaya da shi Asibiti domin yi masa magani yayin da aka ceto yaron.
“Binciken da aka gudanar a wayar wadanda ake zargin ya nuna cewa an sayar da yara 45 da aka sace tare da ddaukar nauyinsu ba bisa ka’ida ba daga wasu jama’a da ba a san ko su waye ba a fadin kasar nan.”