Daya daga cikin marubutan littattafan Hausa na yanar gizo JAMILA UMAR (JANAJFTY) ta bayyana wa masu karatu dalilan da suka sa har ta tsunduma fannin rubutu, tare da bayyana wasu batutuwan masu yawa wadanda suka shafi rayuwarta. Ga dai tattaunawar tare da PRINCESS FATIMA ZARAH MAZADU Kamar haka:
Ya sunan marubuciyar?
Sunana Jamila Umar, Wacce duniyar rubutu da marubuta suka fi sani da Janafty.
Ko za ki fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
A takaice dai ni Haifaffiyar garin Zariya ce da ke Jihar Kaduna, na yi karatuna duka tun daga matakin firamare har zuwa matakin NCE a babban kwalejin kimiyya da fasaha ta zariya wato ‘Federal Collage of Education Zariya’, ban yi aure ba ina zaune tare da iyayena a garin Zariya.
Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma fannin rubutu?
Ba zan iya cewa ga abun da ya ja hankalina na fara rubuce-rubuce ba, abu daya na sani tun ina karamata ina da sha’awar karance-karance, sannan ina son rubutu kuma karatu baya bani wahala. Na fara rubuce-rubuce tun a littafin makarantuna kafin ci gaba ya zo mana na wayar zamanin nan.
Lokacin da ki ka fara sanar da iyayenki kina sha’awar rubutu, shin kin fuskanci wani kalubale daga gare su?
Gaskiya ban fuskanci wani kalubale ta bangaren iyayena ba, daman sun san ni mai son karance-karance da sha’awar rubutu ce, shiyasa sanda na ce musu zan fara rubutu abun bai zo musu a sabon abu ba, sun ba ni cikakken goyon baya, sannan suna bina da fatan alheri a koda yaushe.
Ya farkon fara rubutunki ya kasance?
Gaskiya ban wani fuskanci wata matsala yayin farawata ba, illa ma za a kira wata matsala bai wuce na rashin sabo da Taifin ta waya ba, shi ya dan bani wahala, daga baya kuma da na saba shikenan. Zan iya cewa da kafar dama na shigo duniyar marubuta tunda makaranta da marubuta sun karbe ni da karramawa tun a karon farko. Farkon farawa cike da Nasara ne, na gaya miki ban samu wata matsala a harkan rubutuna yayin farawa ba gaskiya. In ma akwai matsala ita ce; wacce na sanar da ke a baya.
Za ki kamar shekara nawa da fara rubutu?
Zan yi kamar shekara hudu zuwa biyar.
Kin rubuta labari sun kai kamar guda nawa?
Da fara rubutuna kawo yanzu na rubuta labarai guda ashirin.
Wanne labari ne cikin labaran da ki ka rubuta ya zamo bakandamiyyarki?
Labarina na uku mai su NAZIR, kamar zan iya cewa shi ne bakamdamiyata, duk da cewa ina da kyakyawan tabbacin duka Labaraina bakamdamai na ne. amma shi ya zama na dabam ta dalilinsa mutane da dama suka sanni, nima kuma na sansu, sannan sunana ya shiga inda ban taba tunani ko tsammani ba.
Wanne labari ne ya fi baki wahala wajen rubutawa?
Labarin da na rubuta mai suna SADAUKARWAR SO shi ne ya fi bani wahala wajen rubuta shi, ba wani dalili ba ne mai karfi kawai daga baya ne na ji Labarin ya fara fita kaina, sai ya kasance in ina rubutu ba ni da karsasashi da zumudin da na ke tsintar kaina a ciki in ina rubutu.
Ko akwai labarin da ki ka taba bugawa cikin labaranki?
Eh! na buga guda hudu daga ciki.
Wanne irin nasarori ki ka samu game da rubutu?
An samu nasarori kam masu tarin yawan da baki ba zai iya kirga su ba, babban nasarar da zan daki kirji nayi magana a kanta shi ne nasaran samun masoya dake zagaye da duniyata ya fiye min duka girman nasororin da na samu a rubutuna, ba abun da za mu ce sai godiya, Alhamdulillah kawai zan iya cewa.
Ko akwai wani kalubale da ki ka taba fuskanta ga sauran marubuta ko kuma makaranta?
Kalubale kam akwai shi, tunda kowani matakin nasara na ci gaban rayuwa akwai kalubale, kuma baka samun nasara sai ka fara cin karo da kalubale, sai dai nasarorin su suka danne tasirin kalubalen a wajena.
Ya ki ka dauki rubutu a wajenki?
Na dauki rubutu wata saukakkiyar hanya ta isar da sako ko manuniya da hannunka mai sanda zuwa ga al’umma, kin san an ce marubuci kamar madubi ne a cikin Al’umma.
Wanne abu ne ya taba faruwa da ke na farin ciki ko akasin haka wanda ba za ki taba mantawa da shi ba game da rubutu?
In tuna cewa yau rubutuna ya kai kafarsa inda ban je ba, sannan mutanen da suke karanta labaraina mutane ne masu karamci da sanin ya kamata wanda kila ba dan rubutuna ba, ba za su taba sanina ba. Sannan ina jin dadin yadda nake samun yabawa ta kowani bangare a kan labaraina, yabawar da kuma tarin addu’o’i daga bakuna dabam-dabam, kauna tare da soyayyar Masoya gare ni yana sakani cikin jin dadi da alfaharin zamowata marubuciya.
Mene ne burinki na gaba game da rubutu?
Burina shi ne rubutu ya kara daukaka a duniya. Marubuta su sake zama masu daraja wajen Al’umma. Sannan ina so nayi rubutun da zai zagaye duniya gaba daya, inada burin duka rubutuna ya karkata akan mata da irin gwagwarmayan da suke fuskata a rayuwarsu da kuma zamantakewarsu a gidajen aurensu, inada burin sanadin rubutuna mata da yawa su dogara da kansu, su kuma tsaya da kafafunsu.
Kamar wanne lokaci ki ka fi jin dadin yin rubutu?
Na fi jin dadin rubutu da safe haka, sannan na fi jin dadinsa in ya kasance raina a bace yake.
Me za ki ce da masoyanki?
Babu abun da zan ce musu sai godiya, domin da kwarin gwiwansu na kai har iyanzu ana jin sunana, da babu su ni ma da tuni an dade da mantawa da ni, ina alfahari da masoyana su ne Janafty in ba su da tuni sunan Janafty ya dade da shafewa a duniyar yanar gizo. Ina musu addu’a yadda Allah ya hadu a duniya cikin kaunar juna Allah ya kara hada mu a Aljannah masu kaunar juna.
Gaida mutum biyar.
Zan fara da gaida Sisina Aisha Muhammad Alto, sai Hafsah Mustapha Hafnan, sai Zainab Muhammad Chubado, ina gaida Firdausi Fedhoom sai kawata Surayya Dahiru Gwaram.
Muna godiya, ki huta lafiya.
Ni ma na gode.