Babban bankin kasar Sin, ya bukaci a yi kokari daga bangarori daban daban domin saukakawa baki harkokin da suka shafi biyan kudi a kasar.
Yayin wani taro kan inganta hidimomin biyan kudi a jiya, gwamnan babban bankin Pan Gongsheng, ya bukaci a samar da hadaddu kuma ingantattun matakai domin samar da sakamako mai inganci nan ba da dadewa ba.
- Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Kar-ta-kwana Kan Haramtattun Gine-gine
- Gwamnatin Buhari Ita Ce Mafi Muni A Tarihin Nijeriya – Mahdi Shehu
Manhajar Alipay, wadda daya ce daga cikin manhajojin biyan kudi na kamfanin Ant Group, yana ba bakin dake kasar Sin damar amfani da kantin baki na kasashen waje ko kuma amfani da manhajar wajen daukar hoton QR codes domin biyan kudi.
Haka kuma, bankunan kasar Sin na daukar matakan fadada amincewa da katunan banki na kasashen waje domin saukakawa baki wajen amfani da kudi a cikin kasar. (Fa’iza Mustapha)