….Ci gaba daga makon da ya gabata
A wannan makon za mu duba Sarki na 6 a jerin wadanda suka muki masarautar Hadejia.
6. Buhari bin Sambo, 1848-50 zuwa 1851-1863
Abubakar Buhari bin Muhammad Sambo Digimsa shine Sarkin Hadejia na 4 amma bayan shekaru na Jihadi,ya kuma kasance a zamanin mulkinsa ne lokacin da ba za a manta da shi bane musamman ma idan ana maganar tarihin Hadejia.Sambo ya mutu ne a shekarar 1848 kuma sai ta kasance a hannun Buhari, kafin rasuwar mahaifinsa sai abin ya kasance duk wani salon iya mulki an nuna ma sa su maimakon a nuna wa Ahamadu wanda shi Sambo yana ganin shi ne zai gaje shi bayan rasuwarsa.
Duk da yake Buhari ne ya zama Sarkin Hadejia a wata matsalar da aka samu amma amincewa da hawan gadon Sarautar shi daga Sakkwato ne aka samu amincewar hakan.Buhari bai dade da hawa gadon Sarauta ba sai aka kashe dan’uwansa, Nalara Sarkin Auyo,wanda wani al’amari ne da yaba mahukuntan Sakkwato wata dama da suke jira ta cire ta cire Buhari daga gadon Sarauta.
Hakanan ma a shekarar 1850 da yake ba a samu nasarar ta hanyar difilomasiyya ba sai Kalifanci ya ba Wazirin Sakkwato umarni tare da taimakon wasu dakaru daga Katagum domin a dora dan’uwan Buhari Ahmadu a matsayin sabon Sarkin masarautar Hadejia za ayi hakan ne amma idan an samu wata dama.
Daga karshe dai an nada Ahamadu a matsayin Sarkin Hadejia a shekarar 1850 sai kuma Buhari ya koma Machina wato irin al’amarin nan da idan aka fidda Sarkin daga Sarauta ba’a barinsa a garin sai a kai shi wani wuri kamar yadda aka yi ma marigayi Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na 1, zamanin jamhuriya ta farko aka kai shi Katagum shekaar 1950 lokacin da aka nada Ado Bayero matsayin sabon Sarkin Kano.Sai dai kuma wani al’amari na Allah cikin shekara daya ce kawai sai ga Buhari ya sake dawowa Hadejia inda ya fafata a shekarar 1851,bayan samun dakaru masu yawa da kuma kayan aiki wato Kudi ya fuskanci dakarun dan ‘uwansa Ahamadu duk kuwa da yake ya samu taimako daga Katagum, sai ga shi an samu galaba a kan dakarun shi aka kashe Ahamadu a fagen daga ba tare da wata wahala ba.Ta haka ne Buhari ya sake dawowa mulkin Hadejia a matsayin Sarkin ta duk da yake mahukunta na Sakkwato basu so,wannan shi ne mafarin maganar nan da ake yi mata lakabi da adawar Buhari ko abin nan da aka cewa (Taskar Suleiman Ginsau).
Sarkin Hadejia ya yi shekaru goma sha biyar yana matsayin kamar dan tawaye saboda ya cire masarautar Hadejia daga daular Usumaniyya da hedikwatarta ke Sakkwato.Abu daya da yake babbane shine yadda rashin biyayya ko goyon bayan Buhari ga daular Usumaniyya abin ya kara fitowa fili ne a wani artabu da aka yi a kauyen Kaffur.
A shekarar 1853 ce daular Usumaniyya ta sake daukatr wani mataki wanda take ganin zai iya kawo karshen wani Kallon masheka Ayar da ya ke yi mata, domin duk wadansu masarautun da ake yi ma kalon suna da kima an sa su a cikin yakin,amma daga karshe duk sai kidin nasu ya kare a jinjina.