A Nijeriya ana fara shuka Makani ne daga watan Maris zuwa watan Afirilu, wani lokacin kuma daga watan Afirilu zuwa watan Mayu.
Tsawon Wane Lokaci A Girbe Shi?
yadda binciken masana harkokin nomansa ya nuna, Makani na kammala girma ne cikin wata takwas, sannan a daidai wannan lokacin ne ya kamata manomi ya girbe shi.
Idan aka shuka shi a kasar noman da ta dace, ana samun amfani mai dimbin yawa, musamman idan kasar noman ta kasance ta na rike ruwa sosai.
Shin Ana Samun Riba Mai Yawa A Noman Makani A Nijeriya?
Ko shakka babu, ana samun dimbin riba a noman Makani, sannan ribar da ake samu ya danganta da irin kyansa, inda a wani lokaci a kan samu ribar daga Naira 408,608 zuwa Naira 840,000, ko kuma daga Naira 235,592 zuwa Naira 431,392.
Akasari, an fi yin noman Makani a kasar noman da ta bushe; sannan kuma ana gwama nomansa da wasu amfanin gona kamar Masara da waken Soya da kuma Rogo.
Kudaden da ake kashewa wajen nomansa; bai kai wanda ake kashewa a noman Rogo ba.
Yaya Ake Girbin Makani?
Makani na kammala girma ne a watan a takwas, bayan an shuka Irinsa; sannan kuma ana girbe shi ne ta hanyar tugo shi tun daga jijiyarsa ko kuma hako shi daga cikin kasar da aka shuka shi.
Matakan Noman Makani Don Samun Riba A Nijeriya:
Ana samun riba mai yawa a noman Makani, don samun riba a Nijeriya, har ila yau Makani cima ne ga ‘yan Nijeriya da dama; ana kuma yin nomansa a Kudancin kasar nan, ba kuma ya yin girman da ake bukata idan zafin rana ya yi masa yawa ko kuma idan akwai karancin ruwa.
Tsara Yadda Za A Gudanar Da Nomansa Domin Samun Riba:
Ana bukatar tsarinka na noman Makani ya kasance ya kunshi dukkanin abubuwan da ka ke so ka gudanar, domin yin nomansa ta yadda za ka samu cin nasara ba tare da wata tangarda ba.
Gyaran Gonar Da Za Ka Shuka Shi:
Idan za ka noma shi don samun riba, ya kamata ka samu babbar gona ko ka nemi ta haya ko kuma daga gurin hukumomin harkar noma na gwamnati, misali daga ma’aikatar aikin noma da raya karkara ko kuma daga gurin hukumamin kula da koramu.
Bugu da kari, za ka iya yin gyaran gonar ta hanyoyi biyu, wato ta hanyar gargajiya ko a zamanance.
Har ila yau, za ka iya shuka shi a kowane lokaci a shekara, musamman saboda irin yanayin da ake da shi, amma ya fi yin kyau a kudancin Nijeriya.
Lokacin Da Ya Fi Dacewa A Shuka Makani A Kudu Da Yamma Da Gabashin Nijeriya:
A wasu sassa na kasar nan, ana samun ruwan sama mai yawa ana kuma bai wa manomansa shawara ka da su shuka shi a lokacin da ake yin rana sosai, sannan kuma lokacin da ya fi dacewa a shuka shi a kudanci da gabashin kasar nan, shi ne lokacin aka samu matsakaicin ruwan sama.
Ana kuma iya shuka shi a tsakanin watan Mayu zuw watan Afirilu, amma a Arewacin Nijeriya; ana shuka shi a kowane lokaci na damina.
Yadda Ake Samo Irin Makani:
Za a iya sayo Irin Makani a kasuwanin da suke fadin wannan kasa, ana kuma iya samun sa da dama a kasuwannin da ke Jihohin Kuros Riba, Ondo, Enugu, Edo da kuma garuruwan Jos da Abakilike.
Lokacin Da Ya Kamata A Girbe Shi:
Za a iya girbe shi bayan ‘yan watanni, inda manomansa ke tugo shi daga tushensa ko kuma janyo shi daga cikin kasar da aka shuka shi.
Adana Shi Bayan An Girbe Shi:
Za a iya adana shi daga sati hudu zuwa sati shida, musamman ana so yanayin da za adana shi ya kai nauyin ma’aunin yanayi 7°C.