Hukumar kula da ‘yan gudun hijira da bakin haure da ‘yan gudun hijira ta kasa NCRMIDP ta raba wasu kayan abinci ga mata sama da 700 da suka rasa matsugunansu a jihar Katsina.
Kwamishinan tarayya na NCRMIDP, Hon. Tijjani Aliyu Ahmed, ne ya jagoranci tawagar zuwa Katsina domin rabon kudade ga wadanda suka amfana a karshen mako, ya fara ziyarar Gwamna Umaru Dikko Radda a ofishinsa.
- Rundunar Sojin Sama Ta Kashe ‘Yan Ta’adda Da Dama Tare Da Lalata Maboyarsu A Katsina Da Zamfara
- Gwamnati Katsina Ta Kashe Miliyan 50 Wajen Gyara Motocin ‘Yansanda 15
Ahmed ya sanar da gwamnan irin ayyukan da Hukumar ke gudanarwa, musamman shirinta na samar da cibiyoyin horar da ‘yan kasuwa a fadin shiyyoyin kasar nan.
Da yake nuna damuwarsa kan yawaitar ayyukan ‘yan bindiga a jihar da ke kara yawan ‘yan gudun hijira a kullum, Ahmed ya bayyana cewa gwamnati na da shirin bai wa ‘yan gudun hijirar damar dogaro da kansu.
Ya ce tuni Hukumar ta horas da yara kimanin 120 da suka rasa matsugunnansu, yayin da kuma aka bai wa mata 70 jari don samun ingantacciyar rayuwa da gina rijiyoyin burtsasai masu amfani da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a sansanonin su.
Kwamishinan na tarayya ya nemi hadin kan gwamnatin jihar domin a yi amfani da cibiyoyin tsugunar da ‘yan gudun hijira da aka gina kwanan nan, inda ya ce ayyukan ‘yan fashin na ba mutane tsoro.
Ya godewa gwamnatin jihar bisa kokarinta na bayar da tallafi ga ‘yan gudun hijira tare da yaki da matsalar ‘yan fashi a jihar.
Shi ma da yake nasa jawabin, Gwamna Radda, ya godewa hukumar kan goyon bayan da take bayar wa, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa ta riga ta dukufa wajen ganin an shawo kan matsalolin jama’a.
Radda ya kuma shaida cewa, gwamnati ta kulla kawance da hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya UNDP, ciki har da hukumar kula da ‘yan gudun hijira a wani yunkuri na rage matsalolin da ‘yan gudun hijira ke fuskanta da samar da mafita mai dorewa don sake dawo da su tare da karfafa musu guiwa.