Babban Sufeton ‘Yansanda na Kasa, Kayode Egbetokun, ya jaddada aniyar rundunar na samar da ingantaccen tsaro a fadin Nijeriya, bayan fara azumin watan Ramadan.
Sanarwar da kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar a ranar Litinin a Abuja, ta ce Egbetokun ya bayar da tabbacin ne, a yayin da yake mika sakon gaisuwa ga al’ummar Musulmi a yayin da suka tashi da azumin watan Ramadan.
- An Rufe Taro Na Biyu Na Majalisar Wakilan Jama’ar Kasar Sin Karo Na 14
- Ramadan: Hukumar Tace Fina-finai Ta Bayar Da Umarnin Rufe Duk Wani Gidan Gala Da Ke Kano
An ruwaito sanarwar na cewa, “A wannan wata mai tsarki, rundunar ‘yansandan Nijeriya ta kudiri aniyar tabbatar da zaman lafiya, tsaro da walwalar al’ummar kasa.
“Rundunar ‘yansanda a matsayinta na hukuma, ta fahimci muhimmancin mutunta addinai da al’adu da kuma bukatar dabbaka akidun hakuri da fahimtar juna da hadin kai a wannan al’umma mai mabambantan jama’a”.
Babban sufeton ya bukaci al’ummar Musulmi da su rungumi halayen tausayi da yawan kyautatawa da yafewa juna da watan Ramadan ya siffantu da su.
Ya kuma bukaci a samu hadin kai da tallafawa juna, da dabbaka samun zaman lafiya da kaunar juna da abota da hadin kai a watan Ramadan da ma bayansa.
A yayin da yake kira ga al’umma da su rungumi tsarin tsaro a unguwanni, ya bukaci ‘yan Nijeriya da su taimakawa kokarin rundunar wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a watan Ramadan.
Kazalika, ya bukaci al’ummar Musulmi su ci gajiyar albarkar da ke tattare da watan Ramadan sannan su yi kokari wajen kyautata rayuwar wasu.