Shugaban kasa Bola Tinubu ya roki gwamnonin jihohin kasar nan 36 da su fara bai wa ma’aikata kyautar albashi kafin zuwa lokacin da za a kammala tantance mafi karancin albashin za ake biya domin rage wahalhalun da ake fuskanta.
Shugaban ya bayyana cewa, da jihohin sun fara aiwatar biyan kyautar albashi ga ma’aikata, da hakan zai rage radadi da samar da abin da ake bukata.
Da yake jawabi a Minna, babban birnin Jihar Neja yayin bikin kaddamar aikin noma da samar da abinci da kuma kaddamar da gyaran filin jirgin jihar da aka sauyawa suna zuwa ‘Bola Ahmed Tinubu’ a ranar Litinin, shugaban ya bayyana cewa akwai bukatar dukkan jihohin kasar su rungumi tsarin biyan mafi ƙarancin albashi, domin Majalisars Zartarwa ta Tarayya (FEC), ita ma za ta rungumi tsarin.
Har wa yau, shugaban ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba za a fara ba da lamunin dalibai da sauran matakan tattalin arziki yayin da gwamnati ke daukar matakai na kawar da yunwa da matsin rayuwa.
Tinubu ya kuma bayyana tsare-tsaren da yake yi na tunkarar kalubalen hare-haren ta’addanci, satar shanu, da sauran batutuwa masu alaka da tsaro.
Ya yaba da ci gaba da kuma kokarin da gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ke yi wajen inganta noma don samar da abinci gami da kokarin da yake yi na ganin Jihar Neja ta kasance cikin sahun gaba wajen samar da abinci a kasar nan.
Tinubu ya yi alkawarin bai wa jihar goyon baya don tabbatar da samun ingantaccen abinci a fadin kasar nan.