Wani mai sana’ar POS mai shekaru 37 mai suna Mohammed Sani Abdulrahman da yake da zama a Kurnar Asabe Quarters a cikin birnin Kano, ya samu kyautar kudi har Naira N500,000.00 daga hannun wani dan kasuwa, wanda ya yi kuskure ya tura masa Naira Miliyan N10,000,000.00 a maimakon Naira Dubu N10,000.00.
An kai rahoton faruwar lamarin ga ‘yansanda a watan Disamba, 2023 yayin da jami’an rundunar ‘yansandan jihar Kano suka dauki watanni uku kafin su kammala bincike tare da warware lamarin a ranar Laraba, 13 ga watan Maris.
- Ba Za A Iya Dakatar Da Dunkulewar Kasar Sin Ba
- Bude Iyakokin Nijeriya Da Nijar: NIS Ta Dage Takunkumin Shige Da Fice
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan (PPRO), SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya wallafa a shafinsa na Facebook a safiyar ranar Alhamis, ya ce, Mohammed ya kai kansa hedikwatar ‘yansandan jihar ne da ke Bompai, Kano, a watan Disambar 2023 kuma ya bayyana cewa, wani abokin cinikinsa da bai san ko wane ne ba, ya aika da kudi Naira Miliyan N9,990,000:00 zuwa asusun kasuwancinsa maimakon Naira Dubu N10,000:00.
Kwamishinan ‘yansandan jihar Kano, CP Muhammad Usaini Gumel ya yabawa Sani mai POS bisa gaskiya da amana da ya nuna a harkar kasuwancinsa.