Nijeriya babbar kasa ce da take da al’umma masu yawa da suka fi kabilu 250 da suke magana da fiye da harsuna 500 wadanda ko wane daga cikinsu yana alfahari ne da al’adunsa.
Sai dai akwai manyan kabilu uku da suka hada da Hausa Yoruba da kuma Ibo wadanda gaba dayansu su ne suka samar da fiye da kashi 60 na al’ummar Nijeriya.
- Uwargidan Shugaban Kasa Ta Bude Makaranta Ga Matan Da Aka Kora AÂ Manyan Makarantu A Bauchi
- Mene Ne Ainihin Nufin Amurka Kan Philippines?
Al’amarin auren Nijeriya da akwai maganar addini da kuma al’adu, mutane da yawa suna yi ma sha’anin aure Kallon wani babban al’amari ne dake da daraja.
Saboda haka ne yawancin daurin auren ana yin shi ne a wuraren Ibadu inda ake yin bukukuwan addini da kuma sa albarka. Maganar gaskiya shi al’amarin auren Nijeriya yana tare ne da nuna muhimmancin al’adu.
Sha’anin aure yana tafe tare ne da abubuwan da aka gada na iyali wanda ya sha bamban daga wadannan iyalan zuwa wadancan da kuma yadda al’ummar wurin suke, wadanda sukan kasance ne da irin abin da suka gada na abubuwan da suka tashi suka ga ana yi. Bukukuwa, al’adu da kuma abubuwan da al’umma suke sa ran gani, al’amarin aure ya shafi ko kunshi abubuwa masu yawa na rayuwa a Nijeriya inda yake nuna cewa da akwai wurin zaman shi a cikin al’ada.
Dokar Nijeriya ta amince da nau’oin aure masu yawa da suka hada da auren kotu, wanda shine aka sani sosai, sai dai abin da aka fi sani shi ne akwai nau’oin aure hudu wadanda ake yi a Nijeriya. Sun hada da auren da ake yin rajista, auren gargajiya, auren da ake yi a Coci ko majami’a, da kuma auren musulunci wanda akan yi a masallaci ko gidan mahaifan wadda za a aura.
Shi auren gargajiya a Nijeriya ana ba ita wadda za a aura sadaki ne kuma ango ne yake badawa wanda daga bisani kuma za a maido bayan an sa albarka, saboda ita Amaryar za ta fara wata sabuwar rayuwa ce ta iyali, sai dai farashin sadakin yana da yawa.
Bugu da kari, wannan nazari an yi ne tun kafin darajar Naira ta karye irin na wannan lokacin. Don haka, adadin kudi ko dukiyar da aka gani na iya ninninkawa a halin yanzu.
Kabilu Biyar Da Aurensu Ke Da Tsada
Shuwa Arab (Jihohin Borno da Yobe)
Bukukuwan aure na wannan kabila suna da yawa akan yi kwana bakwai ko fiye da haka ana shagulgula. Ango zai bada sulan zinari 12 da kuma Shanu 15 zuwa 100, sai dai yawan Shanu na iya karuwa musamman ma idan tana da kyau sosai ko ta na da ilimin zamani.
Bororo (Jihar Adamawa)
Wanda zai auri ‘yar kabilar Bororo shi Angon sai ya ba mahaifan wadda zai aura Shanu daga 10 zuwa15 wannan yana nufin milyoyin Nairori ke nan, bayan kuma akwai abubuwan da za a bukata ya bada.
Kalabari (Jihar Ribas)
An san ‘yan Kabilar Kalabari da sa kudin auren ‘yarsu da yawa da abubuwan da za a saya fiye da kowace kabila a Nijeriya. Ango ana sa shi ya ba da kudade daban- daban saboda shi bikin auren. Sadakin auren ‘yar kabilar Kalabari yana iya kai wa Naira miliyan daya ko fiye da haka.
Okrika (Jhar Ribas)
Angon ko wanda yake son auren ‘yar kabilar Okrika sai ya yi kasafin akalla Naira 400,000 da zai ba mahaifin yarinyar yayin da ita kuma mahaifiyar zai ba da daga Naira 250,000 zuwa 300,000 hakan ya sa jimillar kudaden sun kai Naira 700,000. Wannan duk ba wani abu ba ne domin kuwa da akwai sauran iyalai kamar yara mata marasa aure, kawayen amarya da suke tsararraki, Kakanni, kannen uba, da kuma ‘yan’uwan mahaifiyar amarya da za a yi musu hidima. Al’amarin auren ‘yar kabilar Okrika wato sadakin ko kudin aure abin na iya kai wa Naira milyan daya da rabi ko fiye da haka.
Ibo
A sashen Ibo an fi yin auren gargajiya, al’ummar wurin sun fi shirya wa irin hakan, shi ya sa zai yi wuya ga mahaifan Amarya su rage kudin da ake biya don kawai su saukaka wa surikinsu. Kayan da za a saya sun bambanta ne daga gari zuwa gari ko unguwa zuwa wata unguwa sai dai akwai wadansu abubuwan da ba a canza su. Wani lokaci shi surukin da za iyi aure yana taimakawa wajen ayyukan da ake yi a garin da zai yi aure, wannan kuma ya danganta ne da irin aikin da za a yi. A wasu wurare farashin yakan bambanta ne saboda wasu abubuwa, kamar matakin ilmin ita Amaryar, irin abin da ta karanta, da dai sauran wasu abubuwa. Saboda hidindimun da ake yi a auren Ibo, da wahala a iya iyakance abin da za a kashe.